Dan El Rufai Ya Fadi Matsayarsa kan Bincikar Mahaifinsa, Ya ba da Shawara
- Bello El-Rufai ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya yi magana kan bincikar gwamnatinsa mahaifinsa da ake yi
- Ɗan majalisar wakilan na Kaduna ta Arewa ya bayyana cewa ko kaɗan yin bincike a gwamnati, ba abu ba ne mara kyau
- Sai dai, ya nuna cewa bai kamata a yi bincike don zalunci ba ko don wani ya ɓatawa mutum rai, inda ya ce hakan ba daidai ba ne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufa’i, ya yi magana kan binciken gwamnatin mahaifinsa, Nasir El-Rufai da ake yi a Kaduna.
Bello El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan ba abu ba ne mara kyau a yi bincike, amma ya kasance ba domin zalunci ake yinsa ba.

Asali: Facebook
Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar BBC Hausa a shirinsu na Mahangar Zamani.

Kara karanta wannan
Dan tsohon gwamna, Bello ya fadi matsayarsa kan rigimar El Rufai da Uba Sani da ake yi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello bai ji daɗin faɗan El-Rufai da Uba Sani
Bello El-Rufai ya kuma yi magana kan rikicin siyasa da ke faruwa tsakanin mahaifinsa da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.
Dan majalisar, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa game da sabanin da ke tsakanin manyan jiga-jigan siyasan guda biyu, ya ce ba shi da ikon shiga tsakani ko sulhunta su.
Ya ce ko kaɗan lamarin bai yi masa daɗi domin shi mutum ne mai son zaman lafiya.
Me Bello ya ce kan bincikar gwamnatin El-Rufai
"Ai bincike ba laifi ba ne, amma indai kana bincike don zalunci, wannan laifi ne kuma wallahi Allah sai ya hukunta ka."
"Ko ni a yanzu idan na gama kujerar nan ana iya bincike, amma kowane mulki ka riƙe wai ka je kana bincike, don zalunci ko don ka burge wani, ko dan ka tozarta wani, ko dan ya ɓata maka, indai bincikenka a bisa zalunci ne, Allah ba zai ƙyale ba."

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100
"Mu musulmai Allah zai yafe maka komai, amma idan ka zalunci wani, sai fa ka neme shi ka ba shi haƙuri."
- Bello El-Rufai
Hadimin Tinubu ya caccaki El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya caccaki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Daniel Bwala ya bayyana cewa El-Rufai sai ya rabu da wani sannan yake iya cin zaɓe, don a yanzu ko kujerar sanata ba zai iya ci ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng