Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Karbi Kwamishinan Ganduje a Jam'iyyar NNPP

Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Karbi Kwamishinan Ganduje a Jam'iyyar NNPP

  • Tsohon kwamishinan shari'a a gwamnatin Abdullahi Ganduje, Barista Haruna Isah Falali, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP
  • Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya karɓi Haruna Isa Falali da kansa a gidansa da ke Abuja
  • 'Yan Kwankwasiyya sun nuna farin ciki da shigowar Falali jam'iyyarsu, suna addu'ar hakan ya haifar da nasara a tafiyarsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP ta ƙara samun ƙarfi bayan sauya sheƙar Barista Haruna Isah Falali zuwa cikinta.

Barista Falali, wanda tsohon kwamishinan shari'a ne a Kano a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje, ya kasance tsohon mai ba da shawara na shari'a ga PDP kafin komawarsa NNPP.

Kwankwaso
Kwankwaso ya karbi tsohon kwamishinan Ganduje zuwa NNPP. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Mai taimaka wa Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso a kafafen yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar 6 ga Fabrairu, 2025 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya karɓi kwamishinan Ganduje

An yi taron karbar Barista Haruna Isah Falali ya gudana ne a gidan Rabi'u Musa Kwankwaso da ke Abuja, inda aka yi maraba da shi cikin jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar a matakin ƙasa, ya bayyana farin cikinsa da sauya sheƙar Falali, yana mai cewa hakan wata alama ce ta ƙaruwa da ƙarfi a jam’iyyar.

An bayyana cewa shigowar Barista Falali wata dama ce da NNPP za ta amfana da ita, musamman duba da kwarewarsa a fannin shari’a da siyasa.

Kwankwaso ya jaddada cewa jam'iyyar NNPP na ci gaba da samun ƙarin shahara a Najeriya, yana mai gode wa waɗanda ke komawa cikinta don ci gaban dimokuraɗiyya.

Me magoya bayan NNPP ke cewa?

Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun bayyana jin daɗinsu bisa samun ƙarin jigo a cikinsu, suna mai cewa hakan wata babbar nasara ce ga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Tsagin NNPP ya yi watsi da zaben sabon shugaban jam'iyya

Wani mai goyon bayan Kwankwasiyya ya ce sun yi matuƙar farin ciki da shigowar Barista Haruna Isah Falali, suna maraba da shi cikin tafiyar.

Wasu daga cikin magoya bayan NNPP sun bayyana fatan cewa shigowar Falali jam’iyyar zai ƙarfafa ta wajen cimma nasara a zabukan gaba.

Addu'ar cimma nasara a jam'iyyar NNPP

Baya ga nuna farin ciki, wasu magoya bayan NNPP sun yi addu’a cewa wannan sauya sheƙa ta zama alheri ga jam’iyyar.

Wasu daga cikinsu sun yi addu’ar Allah ya sanya albarka a tafiyar, kuma Allah ya sa hakan ya taimake su wajen cimma nasarar siyasa.

Jam’iyyun siyasa a Kano na ci gaba da karɓar masu sauya sheka daga jam’iyyu daban-daban, yayin da zaben 2027 ke kara matsowa kusa.

Abba Kabir ya zayarci Rimin Zakara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci yankin Rimin Zakara da aka yi rusau da ya jawo mutuwar mutane.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi jihar da suka shirya kwatowa, ya lissafa nasarorin Tinubu

Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gudanar da ayyukan raya kasa a yankin da suka hada da gina tituna, asibiti, samar da ruwan sha da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng