PDP Ta Kara Hargitsewa bayan an Yi Harbe Harbe a Hedkwatar Jam'iyyar, an Samu Bayanai
- An samu ɓarkewar rikici tsakanin magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da na ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike
- Rikicin ya ɓarke ne a hedkwatar jam'iyyar PDP da ke birnin Port Harcourt a ranar Juma'a, 31 ga watan Janairun 2025
- Faɗan ya samo asali ne bayan magoya bayan ɓangarorin biyu sun yi ƙoƙarin karɓe iko da hedkwatar jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - An gwabza faɗa tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da ake kyautata zaton mabiyan gwamnan jihar Rivers ne, Sir Siminialayi Fubara, da ministan birnin tarayya Abuja, Cif Nyesom Wike.
Magoyan bayan ƴan siyasan biyu sun yi rikicin ne a hedkwatar jam’iyyar da ke birnin Port Harcourt a jiya Juma'a.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce rikicin ya haifar da harbe-harbe a kusa da hedkwatar PDP da ke kan titin babbar hanyar Port Harcourt/Aba a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi harbe-harbe a hedkwatar jam'iyyar PDP
Wasu na ganin cewa harbe-harben sun fito ne daga hannun jami’an tsaro da aka girke domin kula da ofishin tun bayan da kotu ta rushe shugabancin Aaron Chukwuemeka na jam’iyyar PDP a jihar.
Sai dai wasu na ganin cewa ƴan daba ne suka haddasa tashin hankalin.
Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan gwamnan jihar, waɗanda aka kore su daga ofishin jam’iyyar bayan da suka samu nasara a kotu, sun yi ƙoƙarin komawa ofishin a safiyar Juma’a.
Amma kafin su samu shiga, wasu magoya bayan tsohon gwamnan, Nyesom Wike sun isa wurin da gaggawa, lamarin da ya janyo hargitsi.
An bayyana cewa rikicin ya ƙara tsananta yayin da kowanne ɓangare ke ƙoƙarin iko da ofishin jam’iyyar.
Ba da jimawa ba, aka fara jin harbe-harbe, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin tsoro da fargaba.
Gwamna Fubara na taƙun saƙa da Wike
Wannan rikicin na ƙara nuna irin rabuwar kawuna da ake fama da ita tsakanin magoya bayan Gwamna Fubara da na tsohon gwamna Wike, wanda a baya suka kasance a tsagin siyasa guda.

Kara karanta wannan
NNPP ta roki tsohon gwamna ya dawo gare ta bayan barin APC, ta yi misali da Abba Kabir
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rikici a cikin jam’iyyar PDP a jihar Rivers, wanda ke da nasaba da rikicin shugabanci tsakanin ɓangarorin biyu.
Ana sa ran jami’an tsaro da shugabannin jam’iyyar za su ɗauki matakin da zai hana sake faruwar irin wannan rikici a nan gaba.
Rikicin PDP ya ƙara tsananta
A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin shugabanci na jam'iyyar PDP ya ƙara ɗaukar sabon salo a jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan an samu sabon shugaban jam'iyya sakamakon hukuncin da kotu ta yanke biyo bayan ƙarar da aka shigar a gabanta.
Hukuncin kotun dai ya rusa zaɓukan da suka samar da shugabannin jam'iyyar PDP masu biyayya ga ministan birnin Abuja, Nyesom Ezenwo Wike.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng