Rusau: Abba zai Kashe Biliyoyi wajen Yin Asibiti, Tituna, Lantarki a Rimin Zakara

Rusau: Abba zai Kashe Biliyoyi wajen Yin Asibiti, Tituna, Lantarki a Rimin Zakara

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a rusau da aka yi a Rimin Zakara a Kano
  • Mai girma gwamna Ya bayar da umarnin dakatar da duk wani aikin rusa gine-gine da jami'ar Bayero ke yi sai an kammala bincike
  • Gwamnan ya kaddamar da shirin ayyukan raya yankin da suka hada da samar da wutar lantarki, ruwan sha, asibiti da tituna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo bayan rusau da aka yi a yankin.

Rasau da aka yi ya dauki hankali kasancewar ya haddasa mutuwar mutane tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

"Ba za mu bari ba," Lauya, Abba Hikima ya je inda ake harbe mutane wajen rusau a Kano

Abba Kabir
Abba Kabir ya ziyarci Rimin Zakara bayan rusau. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Facebook
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Abba ya fitar da jawabi

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook cewa Abba Kabir ya yi alkawarin ayyuka a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika gwamnan ya gana da iyalan mamatan, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki nauyin iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.

Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa Abba Kabir ya bada umarnin biyan kudin jinyar duk wanda aka jikkata a rikicin.

Gwamnan bai tsaya nan ba, ya rabawa iyalai kayan abinci domin rage musu radadi.

Dakatar da BUK daga Rusau a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi jami’an tsaro da su guji harbin fararen hula da bindiga yayin aiwatar da aikinsu, yana mai cewa ba zai lamunci hakan ba.

Baya ga haka, gwamnan ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin tare da gano wadanda suka da hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

'Za mu dauki mataki': Abin da Sanusi II ya ce da aka kashe mutane wajen rusau Kano

Har ila yau, gwamnan ya kira shugabannin jami’ar Bayero zuwa ofishinsa, inda ya umurce su da su dakatar da duk wani aiki na rusau a yankin Rimin Zakara har sai an gama bincike.

Ayyukan da Abba zai yi a Rimin Zakara

Gwamnan ya kuma sanar da shirin raya yankin Rimin Zakara domin ci gaban al’ummar yankin. Ayyukan da za a aiwatar sun hada da:

  • Samar da wutar lantarki a yankin.
  • Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin samar da tsaftataccen ruwan sha.
  • Gina cibiyar kula da lafiya ta farko domin saukaka harkokin jinya.
  • Gina tituna don inganta zirga-zirga a yankin.

Bugu da kari, Gwamna Abba ya bada umarnin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara domin ya zamo sakada mai gudana ga wadanda suka rasa rayukansu a rikicin.

Magana kan rikicin fili a Kano

Kara karanta wannan

Dan Bello ya magance matsalar ruwa a kauyukan Katsina, ya jefa kalubale ga Buhari

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta shawo kan rikicin da ya shafe sama da shekaru 40 tsakanin al’ummar Rimin Zakara da jami’ar Bayero.

Ya jaddada kudirinsa na samar da mafita mai dorewa da zai amfani bangarorin biyu ba tare da cin zarafin kowa ba.

Martanin mutanen Rimin Zakara ga Abba

Shugaban al’ummar Rimin Zakara, Baba Habu Mikail, ya nuna jin dadinsa da irin kulawar da gwamnan ya nuna, yana mai cewa al’ummar yankin ba za su taba mantawa da hakan ba.

Shi ma shugaban karamar hukumar Ungogo, Tijjani Amiru, ya yaba da matakin gaggawa da gwamnan ya dauka, yana mai cewa Gwamna Abba na da kishin al’ummarsa.

Majalisa ta yi magana kan rusau a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta yi Allah wadai a kan yadda aka gudanar da Rusau a Rimin Zakara.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Majalisar ta bukaci a binciki yadda aka gudanar da rusau a yankin cikin dare wanda hakan ya jawo mutuwar mutane da jikkata da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng