Kwankwaso Ya Yi Rashi: Dan Takarar Gwamna a NNPP Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

Kwankwaso Ya Yi Rashi: Dan Takarar Gwamna a NNPP Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Dan takarar gwamnan NNPP a jihar Oyo, ya watsar da jam’iyyarsa zuwa APC domin haɗa kai da shugabanni su kwace mulki a 2027
  • An rahoto cewa Popoola Olukayode Joshua wanda aka fi sani da POJ ya sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Alhamis, 16 ga Janairu 2024
  • Wannan sauya shekar na zuwa ne yayin da Abdullahi Ganduje ya umarci 'yan APC da su tabbata sun kwato mulkin Oyo daga PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - A wani yanayi da ya nuna rikicin cikin gida da ya mamaye NNPP, Popoola Olukayode Joshua ya fice daga jam’iyyarsa zuwa APC.

Popoola wanda aka fi sani da POJ, shi ne ɗan takarar gwamnan jihar Oyo na jam'iyyar NNPP a babban zaben 2023.

Dan takarar NNPP ya yi magana da ya sauya sheka zuwa APC a jihar Oyo.
Dan takarar gwamnan NNPP a jihar Oyo ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Dan takarar gwamnan NNPP ya koma APC

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Popoola Olukayode Joshua ya sanar da ficewarsa daga NNPP a yayin taron jam’iyyar APC jiya Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ma’aikacin gwamnatin tarayya a sashen ayyukan Legas, POJ ya bar PDP zuwa NNPP domin ya fuskanci Gwamna Seyi Makinde a zaɓen 2023.

Amma bayan shan kaye a zaɓen, shi ne POJ ya yanke shawarar komawa APC daga mazabarsa, gunduma ta 10 da ke karamar hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas.

Oyo: APC ta yi maraba da dan takarar gwamna

An ce shugaban APC na jihar Oyo, Alhaji Abass Olaide, ya yi wa POJ maraba da zuwa jam’iyyar tare da tsofaffin shugabannin NNPP da wasu jiga-jigan APC.

Popoola Olukayode Joshua ya bayyana cewa ya shiga APC domin haɗa kai da shugabannin jam'iyyar don ganin sun kwace mulki daga PDP a zaɓen 2027.

Taron ya samu halartar tsohon shugaban NNPP na jiha, Adegbola Adesesan, da tsohon shugaban karamar hukumar Lagelu, Ade Adewuyi.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya yi bayani bayan 'mika' mulkin Katsina ga PDP

POJ ya amsa kiran Ganduje na kayar da PDP

Tun a watan da ya gabata, shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga 'yan jam’iyyar da su mai da hankali kan tazarcen shugaba Bola Tinubu.

Ganduje ya kuma umarci shugabannin APC a Oyo da su ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da sun karɓo mulkin jihar daga PDP a 2027.

Ya bayyana wannan matsayin ne yayin taro da manyan APC na Oyo da aka gudanar a Abuja, inda ya bada umarnin ƙarfafa tsare-tsare.

Ana ganin wannan kiran na Ganduje ne ya yi tasiri a zuciyar Popoola Olukayode Joshua, wanda yake kokarin ganin ya kawo karshen mulkin Makinde.

Popoola Olukayode Joshua zai fice daga NNPP

Tun kafin wannan ranar, Legit Hausa ta rahoto cewa Popoola Olukayode Joshua, dan takarar gwamnan Oyo karkashin NNPP ya sanar da shirin ficewa daga jam'iyyarsa.

A watan Disambar 2024 ne Popoola ya tabbatar da jita-jitar da ake yadawa na cewa zai fice daga NNPP yayin da ya halarci wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Haka zalika, wasu abokan aikinsa sun tabbatar da wannan lamari, inda suka ce shugaban APC na Oyo, Alhaji Moshood Abas, yana jiran Popoola ya shiga jam’iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.