Gwamna Radda Ya Yi Bayani bayan 'Mika' Mulkin Katsina ga PDP

Gwamna Radda Ya Yi Bayani bayan 'Mika' Mulkin Katsina ga PDP

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa furucin Gwamna Dikko Radda na ambaton jam'iyyar PDP a maimakon APC kuskuren harshe ne
  • Gwamna Radda ya jaddada cewa yana daga cikin manyan mambobin APC tun daga shekarar 2014, kuma yana da cikakken biyayya ga jam’iyyar
  • Gwamnatin jihar ta yi alwashin cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaɓukan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar a ranar 15 ga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta yi karin haske kan wata magana da gwamna Dikko Umaru Radda ya yi a lokacin taron kamfen na zaɓen ƙananan hukumomi a Ingawa.

A yayin yakin neman zaben, gwamna Dikko Umaru Radda ya yi kuskuren ambaton jam’iyyar PDP a maimakon APC.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

Radda
Radda ya gyara kuskuren ambaton PDP maimakon APC. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaulaha Mohammed ne ya wallafa bayanin da gwamnatin ta yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Kaula Mohammed ya bayyana cewa kuskuren harshe wata dabi’a ce ta ɗan Adam kuma ba alamar gazawa ba ce ga biyayyar gwamnan ga jam’iyyar APC.

Radda: 'Kuskure dabi'ar dan Adam ne'

Sanarwar gwamnatin Katsina ta bayyana cewa gwamna Radda yana da tarihin kasancewa cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC tun daga shekarar 2014.

A karkashin haka gwamnatin ta ce kuskuren harshe ba ya nuna canjin ra’ayi ko rashin biyayya ga APC, wani al’amari ne da ke nuna cewa kowa na iya yin kuskure saboda ɗabi’ar ɗan Adam.

Misalin wadanda suka yi kuskure a baya

Gwamnatin jihar ta kawo misalai daga sauran shugabannin duniya da na gida Najeriya, inda take nuna cewa irin wannan kuskuren ba sabon abu ba ne a fagen siyasa.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Ibrahim Kaulaha Mohammed ya ce tsohon Firaministan Birtaniya, David Cameron ya taɓa kuskuren ambaton ƙasar Birtaniya a matsayin “ƙasar Kiristoci” a wani taro.

Ya kara da cewa a Najeriya, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya taɓa ambaton PDP a matsayin APC a lokacin wani jawabi a shekarar 2015.

Haka zalika a yayin yakin zaben 2023, shugaba Bola Tinubu ya yi kurkuren kiran PDP yayin da yake kokarin ambaton APC.

APC ta yi alwashin lashe zaben Katsina

A cewar sanarwar, gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Radda ta jaddada cewa APC za ta samu nasarar lashe zaɓukan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

A cewar gwamnatin, nasarar da za ta samu alama ce ta ƙwazon da jam’iyyar ke yi wajen kawo cigaba mai ɗorewa ga jihar Katsina.

Sanarwar ta kuma ƙara bayyana cewa bai kamata kuskuren harshen ya dauki hankalin jama’a daga manufofin cigaba da jam’iyyar APC ke yi wa jihar Katsina ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Maimakon haka, ya kamata a mayar da hankali kan nasarorin da gwamnatin jihar ke cimmawa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

Buhari ya halarci taron APC a jihar Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron masu ruwa da tsaki na APC a jihar Katsina.

A yayin taron, tsohon shugaban kasar ya bukaci shugabanni da su rika tsayar da adalci a Najeriya domin kawo cigaba da bunkasa tattali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng