Rashin Lafiyar Buhari Na Wata Takwas Ya Kawo Wa Mulkinsa Cikas, Adesina

Rashin Lafiyar Buhari Na Wata Takwas Ya Kawo Wa Mulkinsa Cikas, Adesina

  • Fadar shugaban ƙasa ta bayyana illar da rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari ta jawo a gwamnatinsa
  • Femi Adesina yace watanni 8 da Buhari ya yi a Landan ya jawo koma baya a harkokin gwamnati mai ci
  • Kakakin shugaban ƙasan ya maida martani ga Malamin Cocin Katolika da ke Sakkwato, Matthew Kukah

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta ce rashin lafiyar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kwashe watanni 8 yana fama da ita a 2017 ta kawo naƙasu a tafiyar gwamnatinsa.

Mista Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana haka a cikin shirin Politics Today na Channels tv yayin da yake ambato wasu nasarorin gwamnatin Buhari.

Femi Adesina.
Rashin Lafiyar Buhari Na Wata Takwas Ya Kawo Wa Mulkinsa Cikas, Adesina Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a 2017, shugaba Muhammadu Buhari ya tafi ƙasar Burtaniya neman lafiya, inda ya shafe jumullar watanni Takwas a birnin Landan.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

Yayin da aka tambaye shi ranar Litinin 10 ga watan Afrilu, 2023 kan ko rashin lafiyar Buhari ta kawo koma baya a gwamnati, Adesina ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kwarai kuwa ya kamata haka ta faru saboda ya fara rashin lafiya a watan Janairu 2017, ya dawo gida a watan Maris, kana ya koma a watan Afrilu kuma ya dawo ranar 19 ga watan Agusta."
"Jimulla kusan watanni 8 kenan, wannan rashin lafiya ta laƙume watanni Takwas a cikin lokacinsa na mulki. Tabbas babu wanda zai so haka amma mun ji daɗi da ya dawo da kwarinsa fiye da yadda ya tafi."

Adesina ya maida martani ga Kukah

Haka nan a wannan hira, kakakin shugaban ƙasan ya musanta sukar da babban malamin Cocin Katolika na Sakkwato, Matthew Kukah, ya yi kan shugaba Buhari.

A rahoton Vanguard, Adesina ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Bayan Ƴan Bindiga Sun Kashe Rayuka 134 a Watan Azumi, Gwamnan Arewa Ya Roƙi Buhari Muhimmin Abu

"Irin waɗan nan abubuwan bai dace da kamilin mutum mai ilimi kamar Kukah ba, muna ganin girmansa amma yanzu ya shafa wa kalamansa Fentin siyasa."
"Ya yi magana kan sayar da jirgin shugaban ƙasa, shin wani alƙawari ne da aka ɗauka? A 2015, akwai alƙawurran da aka ɗauko ko shi kansa ɗan takarar bai da masaniya."

A wani labarin kuma Daga Karshe, Babban Dalilin Da Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye Hannun Tinubu Ya Bayyana

Sanatan PDP daga jihar Ebonyi ta tsakiya ya ce Atiku ya cancanci ya sha kaye hannun Tinubu saboda rashin kataɓus din NWC.

Sanata Agba ya ce bai kamata PDP ta dakatar da kowa illa nambobin kwamitin gudanarwa tun daga shugabansu, Iyorchia Ayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel