Tsohon Ministan IBB Ya Gargadi Bola Tinubu kan Fito na Fito da Donald Trump
- Farfesa Bolaji Akinyemi ya shawarci shugaba Bola Tinubu da ya guji rikici da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump
- Bolaji Akinyemi ya bayyana cewa rikici da shugaba mai son fada kamar Donald Trump zai iya haifar da illa ga Najeriya
- Sabon salon shugabancin Trump na kunshe da manufofin da Farfesa Akinyemi ya kira masu tsanani ga duniya baki daya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fitaccen masanin kimiyyar siyasa, Farfesa Bolaji Akinyemi ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kauce wa duk wani rikici da sabon shugaban Amurka, Donald Trump.
Akinyemi, wanda ya taba shugabantar Hukumar Kula da Harkokin Duniya ta Najeriya (NIIA), ya bayyana jawabin rantsuwar Trump a matsayin abin takaici da rashin kwarin gwiwa.

Asali: Facebook
Da yake magana a shirin gidan talabijin na Channels ranar Litinin, Akinyemi ya bayyana cewa Trump na da halayen da suka fi karkata ga takaddama da fada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesan ya bayyana cewa manufofinsa na iya kawo wa duniya matsaloli a cikin shekaru hudu na shugabancinsa.
An shawarci Tinubu kan rikici da Trump
Farfesa Akinyemi ya bayyana cewa Tinubu ya kamata ya yi kokarin kauce wa duk wata muhawara da Trump, musamman idan manufofinsa sun shafi Najeriya.
“Idan zan ba Tinubu shawara, ba ta wuce cewa ya guji tsoma kansa cikin rikici da shi (Trump) ba,”
- Farfesa Akinyemi
Ya kara da cewa,
“Trump mutum ne mai son fada da wadanda ba za su iya mayar da martani ba. Idan mutum ya dauki irin wannan gwagwarmaya da shi, zai gamu da karin matsala.”
Farfesan ya yi nuni da karin maganar Afirka da ke cewa, idan mutum ba shi da karfi ya tunkari mai fada, zai kara cutuwa.
Ya kuma bayyana cewa akwai hanyoyi daban-daban na magance irin wannan yanayi ba tare da rikici ba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Akinyemi: Manufofin Trump na da tsauri
Akinyemi ya yi Allah wadai da jawabin rantsuwar Trump, yana mai cewa ya fi karkata ga yin barazana ga duniya maimakon ya nemi zaman lafiya.
Farfesan ya ce;
“Trump ya bayyana shirinsa na dawo da ikon Panama Canal, sake wa Gulf of Mexico suna zuwa Gulf of America, da kuma kaddamar da takaddamar tattalin arziki da sauran kasashe.”
Ya kara da cewa irin wadannan manufofi za su fuskanci martani daga sauran kasashen duniya, yana mai cewa shekaru hudu na mulkin Trump za su kasance masu cike da kalubale.
A cewarsa, Najeriya ba ta cikin jerin abubuwan da Trump ke maida hankali kansu. Don haka, kasar ba za ta samu wani abin kirki daga shugabancinsa ba.
Rantsuwar Trump a matsayin shugaba na 47
Donald Trump ya karbi mulki daga Joe Biden a ranar Litinin bayan shafe shekaru hudu da ya yi a gefe bayan faduwar takararsa ta wa’adi na biyu a shekarar 2020.
Trump, wanda ya fara shugabanci a shekarar 2017 a matsayin wanda ba dan siyasa ba, ya koma mulki a wannan karo.
Wadanda suka halarci rantsar da Trump
Fitattun mutane kamar Elon Musk, Mark Zuckerberg, Jeff Bezos, da Sundar Pichai sun samu guraben zama a Capitol tare da dangin Trump da sauran jami'ai.
Yayin da Trump ya kaurace wa rantsuwar Biden a 2021 saboda zargin magudi, a wannan karo Biden ya halarci taron tare da tsofaffin shugabanni Barack Obama, George W. Bush, da Bill Clinton.
Duk da haka, tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Michelle Obama, ba ta halarci bikin rantsuwar ba, abin da ya kara jawo hankalin jama’a.
Faransa za ta tallafa wa Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Faransa ta shirya horas da 'yan Najeriya fasahar ma'adinai a wannar shekarar.
Ma'aikatar harkokin ma'adinai Najeriya ce ta fitar da sanarwar tare da bayyana cewa za a cigaba da taro tsakanin kasashen biyu a wata mai kamawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng