Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Gwamna Ya Masa Alkawarin Ƙuri'u a 2027
- Gwamna Monday Okpebholo ya tabbatar da cewa jihar Edo za ta ba shugaban ƙasa Bola Tinubu ƙuri’u 100% a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Okpebholo ya bayyana cewa ƙauna da tallafin da Tinubu ke ba masu rauni zai sa duk wani mai katin zaɓe ya dangwala masa a zaɓe na gaba
- Uwargidar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta kaddamar da shirin rabon kayan abinci na RHI a Birnin Benin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya tabbatar wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa masu zaɓen jihar za su ba shi kashi 100 cikin 100 na ƙuri’unsu a 2027.
Gwamma Okpebholo ya bayyana cewa gaba ɗaya masu ƙatin zaɓe a Edo za su zaɓi Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 saboda taimakon da yake wa talakawa.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Asali: Twitter
Monday Okpebholo ya bayyana hakan ne ranar Litinin da yake jawabin godiya a taron kaddamar da shirin sabunta fata (RHI), kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bola Tinubu ta kirkiro shirin RHI
Shirin RHI wani tsari ne na tallafi da rabon kayan abinci ga mabukata kuma an yi taron ne a sabon ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Birnin Benin, jihar Edo.
An fara shirin rabon kayan abincin RHI a ranar 8 ga Maris, 2024, kuma jihohi bakwai sun ci gajiyar shirin zuwa yanzu.
Jihohin sun haɗa da Kano, Benuwai, Nasarawa, Ekiti, Kuros Riba, Gombe, da Edo, sannan ana sa ran zana faɗaɗa shi zuwa jihohi uku, Kwara, Kogi, da Abia nan gaba.
Gwamna ya sha alwashin ba Tinubu kuri'un Edo
Okpebholo ya yabawa uwargidar shugaban ƙasa kuma shugabar RHI, Sanata Oluremi Tinubu, saboda ƙauna da yadda take ɗaukar kowa ɗanta.
Ya ce uwargidar shugaban kasa na taka rawar mahaifiya wajen tabbatar da cewa al’ummar Najeriya sun amfana da romon dimokuraɗiyya.
Ya jaddada cewa ba za a samu nasarar wannan shiri na matar shugaban ƙasa ba, ba tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ba.
Bisa haka gwamnan ya yi alƙawarin cewa gaba ɗaya mutanen Edo za su goyi bayan Tinubu ya yi tazarce a 2027.
Okpebholo ya ce:
“Mun ji daɗi sosai da mutanen Edo suka fara ganin sabon canji, ku duba kayan abinci ta ko ina a wannan daki, muna godiya ga shugaban ƙasa da matarsa bisa wannan shiri da talakawa za su fara amfana daga yau.
“Muna tabbatarwa mai girma shugaban kasa cewa ƙuri’un Edo 100% na shi ne a 2027. Idan ma zai yiwu, za mu ba ka fiye da kashi 100 cikin 100.”
Matar Tinubu za ta faɗaɗa rabon abinci
A nata jawabin, uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Tinubu, ta bayyana cewa an fara shirin rabon kayan abincin a watan Maris 2024, kuma jihohi bakwai sun amfana.
Oluremi wacce matar mataimakin shugaban ƙasa, Nana Shettima ta wakilta a taron, ta ce za a faɗaɗa shirin rabon kayan abincin zuwa jihohi uku.
Dalilin dakatar da ciyamomi a jihar Edo
Kun ji cewa Gwamna Okpebholo ya zargi ciyamomin ƙananan hukumomin jihar Edo da azurta shugabannin jam'iyyar PDP da kuɗin baitul-mali.
Mai girma Monday Okpebholo ya yi ikirarin cewa dakatattun shugabannin ƙananan hukumomin sun tura Naira biliyan 12 ga jagororin PDP a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng