Buhari, Radda da Manyan 'Yan Siyasa Sun Yi Taron Neman Nasara ga APC

Buhari, Radda da Manyan 'Yan Siyasa Sun Yi Taron Neman Nasara ga APC

  • Gwamna Dikko Radda ya umarci shugabannin APC su tashi tsaye domin samun nasara a zaɓen kananan hukumomin jihar
  • Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni da su tabbatar da gaskiya da adalci a shugabancinsu
  • Rahotanni sun nuna cewa manyan jagororin siyasa a jihar Katsina sun haɗu domin ƙarfafa APC da shirya wa zaɓen da ke gabansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga shugabannin jam'iyyar APC da su ƙara himma wajen nemawa APC nasara a zaɓen kananan hukumomi a jihar.

Wannan kira ya fito ne a taron shugabannin jam'iyyar APC da aka gudanar a dakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa a Katsina.

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Buhari
Jiga jigan APC sun yi taro a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin adalci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar da Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, taron ya samu halartar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da sauran manyan shugabannin siyasa na jihar Katsina.

Radda ya tattauna kan muhimmancin adalci

Gwamna Dikko Radda ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da adalci a zabukan da za a gudanar.

Ya bayyana cewa APC tana da burin tabbatar da tsarin dimokraɗiyya da zai ƙarfafa haɗin kan jama’a da bunƙasa jihar Katsina.

Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damawa da jihar Katsina wajen ba ta mukamai a gwamnatinsa ta tarayya.

Shugaba Buhari ya bukaci a yi adalci

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni su kasance masu gaskiya da adalci a dukkan matakai.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya yi bayani bayan 'mika' mulkin Katsina ga PDP

Muhammadu Buhari ya ce irin wannan dabi’a ce ke sa shugabanni su ci gaba da samun girmamawa daga jama’a.

Buhari ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda gwamnatin Gwamna Radda ke tafiyar da al’amuran jihar cikin gaskiya da nuna damuwa kan bukatun al’umma.

Hakazalika, shugabannin jam’iyyar APC kamar Ahmed Musa Dangiwa da Hon. Hanatu Musa Musawa sun yabawa gwamnatin Katsina bisa kyakkyawan shugabanci.

Tattaunawar manyan jagororin Katsina

Taron ya samu halartar tsofaffin gwamnoni biyu na jihar Katsina, Aminu Bello Masari da Ibrahim Shehu Shema, tare da tsofaffin mataimakan gwamnoni Alhaji Sirajo Umar Damari da Abdullahi Garba Faskari.

Haka kuma, manyan 'yan majalisun dattawa irin su Sanata Abdulaziz Yar Adua, Sanata Muntari Dandutse, da Sanata Nasiru Sani Zangon Daura sun halarci taron.

Taron ya hada da fitattun ‘yan siyasa irin su Hon. Abdullahi Jabiru Tsauri, Dahiru Barau Mangal, da Hon. Abbas Masanawa, wadanda suka yi alkawarin marawa APC baya.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Shirin APC na samun nasara a Katsina

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Sani Aliyu Daura, ya bayyana cewa taron ya biyo bayan bukatar ƙarfafa haɗin kan jam’iyya da shirya tunkarar zaben kananan hukumomi.

Ya ƙara da cewa haɗuwar manyan jagororin jihar ya nuna cewa APC na shirye-shiryen cin gagarumar nasara a zaɓen kananan hukumomi mai zuwa.

2027: Matasa sun goyi bayan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa masu matasa a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur sun ce shugaba Bola Tinubu na samun karbuwa.

Kungiyoyin matasa sama da 20 ne suka bayyana haka, inda suka ce shugaban kasar ba zai samu adawa mai karfi ba a zaben shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng