Gwamna Radda Ya Yi Ɓaram Barama a Siyasar APC, Ya Saki Layi a gaban Ganduje

Gwamna Radda Ya Yi Ɓaram Barama a Siyasar APC, Ya Saki Layi a gaban Ganduje

  • Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya yi subutar baki a wurin kaddamar da kamfen APC wanda shugaban jam'iyya na ƙasa ya halarta
  • Da yake jan hankali ƴan APC su tashi tsaye, Gwamna Radda ya yi kuskuren cewa Katsina ta PDP ce kuma za ta ci gaba da zama a inuwar PDP
  • Gwamnan ya yi saurin gyara kalamansa kuma shugaban jam'iyya, Dr. Abdullahi Ganduje ya jaddada cewa Katsina ta jam'iyyar APC mai-ci ce

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya yi tuntuɓen harshe a wurin taron kaddamar da yaƙin neman zaben ƴan takarar APC a zaɓen kananan hukumomi.

Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya halarci taron wanda aka miƙawa ƴan takarar ciyaman a kanann hukumomi 34 tutar jam'iyya.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

Dikko Radda a taron kamfe.
Gwamnan Katsina ya yi subutar baki a wurin kamfen ƴan takarar APC a zaben kananan hukumomi Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammed
Asali: Facebook

Sakataren watsa labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Muhammed ya bayyana yadda taron ya gudana a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya saki layi a taron

Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa Gwamna Raɗɗa ya tafka kuskure a jawabin da ya yi, inda aka ji ya ce jihar Katsina ta PDP ce.

Yayin da yake kira da ƴan APC su tashi tsaye su tallata jam'iyyarsu domin tunkarar zaben ciyamomin, Dikko Raɗɗa ya sauka daga layi, ya ce Katsina ta PDP ce.

"Jihar Katsina na karkashin PDP kuma za ta ci gaba da zama a inuwar jam'iyyar PDP," in ji Dikko.

Dikko Raɗɗa ya yi hanzarin ankara da kalamansa

Cikin hanzari, mai girma gwamnan ya kyara kalamansa to amma duk da haka hakan ya ja hankalin mutane musamman ƴan adawa.

Duk da wannan kuskure, Gwamna Radda ya tabbatar da cewa APC ta ɗauri ɗamar ci gaba da jan zarenta a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

"Mun shirya zuwan zaɓukan da ke tafe kuma ina da ƙwarin guiwar cewa APC za ta lashe zaɓen 2027. Katsina a haɗe take wuri guda karkashin inuwar APC."

Shugaban APC, Ganduje ya gyarawa gwamna

A nasa jawabin, shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gyara kuskuren da gwamnan ya yi, yana mai cewa Katsina ta APC ce.

Ganduje ya ce dumbin mutane da suka hallara a wurin taron da ƴan siyasa sama da 40,000 da suka sauya sheka zuwa APC kaɗai sun isa zama hujja kan inda jihar ta karkata.

“Yawan jama’ar da suka fito a yau, ciki har da masu sauya sheka 40,000 da suka shigo cikinmu, ya nuna cewa Katsina ta APC ce.
"Muna kara ƙarfi, haɗa kai da kuma maida hankalin kan gina shugabani na gari," in ji Ganduje.

APC ta rasa manyan ƙusoshi a jihar Osun

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta gamu da koma baya a yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Osun a 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya yi bayani bayan 'mika' mulkin Katsina ga PDP

Ƴan tawagar tsohon gwamnan jihar kuma minista a mulkin Muhammadu Buhari, Rauf Aregbesola sun sanar da ficewa daga APC, sun ce za su karɓe mulkin Osun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262