Gwamna Ya Rusa Hukumar Zaɓe da Wasu Hukumomin Gwamnati, Ya Sallami Ma'aikata
- Monday Okpebholo ya ci gaba da yin tankaɗe da rairaya a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Edo tun bayan hawa mulki
- A wata sanarwa da sakataren gwamnatin Edo ya fitar, gwamnan ya rusa hukumar zaben jihar da wasu hukumomin gwamnati
- Gwamnan ya umarci shugabanni da mambobin hukumomi su miƙa dukkan kayan gwamnati da ke hannunsu ga babban ma'aikacinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Gwamna Monday Okpebolo, ya rusa hukumar zabe mai zaman kanta ta Edo da wasu hukumomin gwamnatin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Edo, Umar Musa Ikhilor ya fitar kuma aka rabawa manema labarai ranar Talata a Benin.

Asali: Facebook
Gwamna Okpebholo ya rusa hukumomi a jihar Edo
Daily Trust ta tattaro sauran hukumomin da Gwamna Okpebholo ya rusa wanda suka haɗa da hukumar kula da harkokin man fetur da gas ta jihar Edo.

Kara karanta wannan
Gwamnoni sun shiga alhini, sun yi ta'aziyyar mutuwar mutane a hadarin jirgin Binuwai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun kunshi hukumar kula da gandun daji ta jihar, hukumar kula da harkokin Majalisar dokoki, hukumar bincike da hukumar shari'a ta Edo.
Gwamna Okpebholo ya umarci shugabannin hukumomin da sauran ƴan majalisar gudanarwa su miƙa dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu su bar ofis.
Gwamnan Edo ya sallami shugabannin hukumomi
Sanata Monday Okpebholo ya buƙaci su miƙa kayan gwamnati ga babban ma'aikacin gwamnati da ke hukumar, sannan su kama gabansu, cewar The Nation.
"Muna sanar da jama’a cewa mai girma gwamna, Sanata Monday Okpebolo ya amince da rusa dukkanin hukumomin da ke karƙashin gwamnatin jihar Edo ba tare da bata lokaci ba."
“Saboda haka, ana umartar dukkan shugabanni da mambobi da su mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga babban jami’in gwamnati a hukumar da suke,” in ji sanarwar.
Gwamna Edo zai biya albashin watan 13
A wani rahoton, mun kawo maku cewa gwamnan Edo ya ba da umarnin biyan ma'aikata albashin watan 13 saboda su yi shagalin Kirismeti cikin walwala.
Shugaban ma'aikatan gwamnatin Edo ya ce ƙarin albashin wata guda a shekara da gwamnatin ya yi zai ƙara zaburar da ma'aikata wajen sauke haƙƙin da ke kansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng