Yayin da Ake Kukan Tsadar Kujerar Hajji, Tinubu Ya Tausaya da Tallafin Biliyoyi

Yayin da Ake Kukan Tsadar Kujerar Hajji, Tinubu Ya Tausaya da Tallafin Biliyoyi

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tallafa da makudan kudi a harkokin aikin hajji saboda tsadar kujera a bana
  • Mataimakinsa, Kashim Shettima ya bayyana haka inda ya ce shugaban ya tallafa da N90bn domin saukakawa maniyyata
  • Shettima ya fadi haka a yau Laraba 15 ga watan Mayu a birnin Kebbi yayin kaddamar da jigilar maniyyata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce Shugaba Bola Tinubu ya agaza kan tsadar kujerar hajji.

Sanata Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya tallafa da N90bn domin rage tsadar kujerar a wannan shekara da muke ciki.

Tinubu ya tallafa da N90bn domin saukaka kujerar aikin hajji
Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya ba da tallafin N90bn a aikin hajjin bana. Hoto: Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Asali: Facebook

Tallafin Bola Tinubu a ɓangaren aikin hajji

Kara karanta wannan

Bulaliyar kan hanya: Tinubu, Shettima za su fara biyan harajin fakin a filin jirgin sama

Kashim Shettima ya bayyana haka ne yayin kaddamar da fara jigilar maniyyata a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke jihar Kebbi, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an samu tsadar kujerar bayan farashin dala ya yi tashin gwauron zabi idan aka kwatanta da na Naira, Daily Nigerian ta tattaro wannan.

Hari ila yau, Shettima ya ce Tinubu yana aiki ba dare ba rana wurin inganta farashin Naira domin tabbatar da sauki ga maniyyata da sauran jama'a.

Shugaba Tinubu ya dukufa wurin inganta Najeriya

"Idan ba ku manta ba, mun fuskanci kalubale wurin sanar da farashin kujerar hajji saboda yanayin farashin dala."
"Tinubu ya na aiki tukuru wurin inganta darajar Naira da kuma saukakawa maniyyata da sauran al'umma."
"Hakan ya sake rage farashin kujerar inda Tinubu ya tallafa da N90bn domin saukakawa maniyyata."

Kara karanta wannan

Ba a gama da matsalar gida ba, Tinubu ya yi alkawari ga shugaban Chadi, Deby

- Kashim Shettima

Shettima ya ce gwamnatinsu ta himmatu wurin inganta harkokin aikin hajji a kokarinta na dabbaka bangarori da suka shafi tarbiyya da addini.

Tinubu, Shettima za su biya haraji

A wani labarin, an ji Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima za su fara biyan haraji a filayen jiragen saman Najeriya.

Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 14 ga watan Mayu a Abuja bayan taron Majalisar zartarwa.

Keyamo ya ce tun farko dokar ba ta shafi shugaban kasa da mataimakinsa ba sai da Tinubu ya tilastawa kansa da sauran mukarrabansa biyan kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel