Bulaliyar Kan Hanya: Tinubu, Shettima Za Su Fara Biyan Harajin Fakin a Filin Jirgin Sama

Bulaliyar Kan Hanya: Tinubu, Shettima Za Su Fara Biyan Harajin Fakin a Filin Jirgin Sama

  • Yayin da ake korafe-korafen kan ƙaƙaba haraji da gwamnatin Bola Tinubu ke yi, shugaban bai ware kansa ba a kan lamarin
  • Tinubu ya soke dokar da ta hana shi da mataimakinsa, Kashim Shettima biyan harajin a filayen jiragen saman kasar yayin shiga
  • A zaman majalisar zartarwa a yau Talata 14 ga watan Mayu, an tabbatar da cewa Tinubu da Kashim za su fara biyan kudin fakin a filin jirgi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ba su tsira daga biyan haraji ba a Najeriya.

Tinubu da Shettima za su biya kudin fakin a dukkan filayen jiragen sama a Najeriya kamar yadda kowa ke biya.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta maka kakakin Majalisa a kotu kan shirin aurar da mata marayu 100

Tinubu, Kashim ba su tsira daga biyan haraji ba a Najeriya
Sabuwar doka ta kakabawa Bola Tinubu da Kashim Shettima biyan harajin fakin da shiga filayen jiragen sama. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Ƙashin Shettima.
Asali: Facebook

Dokar da aka ƙaƙaba kan Tinubu, Shettima

Wannan ya biyo bayan zaman majalisar zartarwa kan kin biyan haraji da wasu manyan jami'an gwamnati ke yi a filayen jiragen sama, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo shi ya bayyana haka a yau Talata 14 ga watan Mayu yayin ganawa da manema labarai.

Keyamo ya ce Najeriya na asarar akalla 82% na kudaden shiga da ake samu yayin shiga filayen jiragen saman kasar.

Tun farko dokar ta ware shugaban kasa da mataimakinsa amma Bola Tinubu ya soke wannan doka daga yau, cewar rahoton TheCable.

Tinubu ya tilasta kowa biyan haraji

Tinubu ya ce da shi da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran hadimansu za su ci gaba da biyan wadannan kudi.

"Dokar ta ce ban da shugaban kasa da mataimakinsa, amma Shugaba Tinubu ya fi karfina, ya ce shi da mataimakinsa za su biya kowa ma zai biya kudin."

Kara karanta wannan

Ba a gama da matsalar gida ba, Tinubu ya yi alkawari ga shugaban Chadi, Deby

- Festus Keyamo

Keyamo ya ce manyan jami'an gwamnati da suke da kudi ba su biyan harajin wanda hakan ya saka hukumar tatsar kudin a hannun talakawa.

Tinubu ya dakatar da harajin CBN

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya dakatar da biyan harajin tsaron yanar gizo a Najeriya da aka kakabawa 'yan kasar.

Tinubu ya dauki matakin ne bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kawo tsarin biyan harajin 0.5% kan masu tura kudi bankuna.

Shugaban ya ce bai kamata a ƙaƙaba wannan haraji a dai-dai wanan lokaci da 'yan ƙasar ke cikin wani hali ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel