Tsohon Gwamnan PDP Zai Koma Jam'iyyar APC? an Fayyace Gaskiya Kan Lamarin

Tsohon Gwamnan PDP Zai Koma Jam'iyyar APC? an Fayyace Gaskiya Kan Lamarin

  • Yayin da ake ta yaɗa jita-jitar zai bar PDP, tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu ya yi martani kan labarin
  • Ikpeazu ya yi fatali da jita-jitar inda ya ce kwata-kwata bai taba tunanin barin jam'iyyar PDP ba inda ya ce zai sake gina ta
  • Hakan ya biyo bayan sauya sheka zuwa APC da wasu jiga-jigan PDP da hadimansa suka yi a jihar a wannan mako

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Tsohon gwamnan jihar Abia, Dakta Okezie Ikpeazu ya yi martani kan jita-jitar cewa ya na shirin komawa APC.

Ikpeazu ya ƙaryata maganar inda ya ce ko kusa babu wani shirin da ya ke da shi na barin jam'iyyar PDP tare da komawa APC, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan Kaduna, Gwamnan APC ya zargi uban gidansa da yashe lalitar gwamnati gaba ɗaya

Tsohon gwamnan PDP ya yi martani kan komawa jami'yyar APC
Tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu ya ƙaryata shirin barin PDP tare da komawa APC. Hoto: Umar Ganduje, Okezie Ikpeazu.
Asali: Twitter

Musabbabin da ya sa ba zai bar PDP ba

Ya ce gwara ya tsaya a jami'yyarsa ta PDP domin ci gaba da gina ta donin ta kara karfi a jihar da ma kasar baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar a birnin Umuahia na jihar Abia.

Ya bukaci mambobin jam'iyyar da su hada kai domin tabbatar da jam'iyyar ta dawo kan gajiyarta na cin zabe a Najeriya.

Ya kara da cewa sauya sheka da wasu hadimansa suka yi da sauran jiga-jigan jam'iyyar wannan ra'ayinsu ne, cewar New Telegraph.

Ya shawarci wadanda suka ci gajiyar PDP

"Dole mu dauki laifin duk abin da ya faru a zaben 2023, jam'iyyar PDP ta na cikin yanayin sake tsaftace kanta ne."
"Babu abin da zai saka ni barin PDP, ina nan daram a PDP domin ci gaba da gina ta yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

"Duk wadanda ke son tafiya za su tafi duk yadda ka yi, amma dai biyayya ga jam'iyyar ya na da kyau musamman wadanda suka ci moriyarta."

- Okezie Ikpeazu

Tsohon Sanata da Minista sun koma APC

A baya, kun ji cewa tsohon Sanata a jihar Enugu, Chuka Utazi da tsohuwar Ministar Sufuri sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Sannan dan takarar jam'iyyar LP a zaben gwamnan jihar da sauran jiga-jigan jami'yyun PDP da APGA sun watsar da jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel