Gwamnan PDP Ya Ɗauki Zafi Kan Rikicinsa da Ministana Tinubu, Ya Faɗi Dalilin Amincewa da Sulhu

Gwamnan PDP Ya Ɗauki Zafi Kan Rikicinsa da Ministana Tinubu, Ya Faɗi Dalilin Amincewa da Sulhu

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya ce bai bari rikicin siyasar jihar Ribas ya yi kamari ba saboda shi mutum ne mai mutunci da girmama na gaba
  • Fubara ya tuna yadda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kira kowane ɓangare da ke faɗa da juna a Abuja kuma ya sulhunta su
  • Gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa idan yarjejeniyar zaman lafiyar da ya amince da ita a ƙarshen 2023 ragwanta ne, "zan ba su mamaki"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya gargadi masu sukarsa da kada su kuskura su kai shi bango.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Fubari ya ƴi wannan jan kunnen ne yayin da ya karɓi bakuncin kungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi (NULGE).

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya bayyana inda aka kwana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Wike, Bola Tinubu da Gwamna Fubara.
Gwamna Fubara ya shirya murkushe masu ganin aibunsa Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

NULGE daga dukkan ƙananan hukumomi 23 sun ziyarci gwamnan domin nuna masa goyon baya a gidan gwamnati da ke Fatakwal ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya sa Fubara ya amince da sulhu

Gwamnan Ribas ya bayyana cewa ya yanke shawarar fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ne kawai saboda yana mutunta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

A ruwayar Channels tv, Gwamna Fubara ya ce:

"Bari na yi magana a nan saboda ya zama hujja, abin da ke faruwa a jiharmu ba komai bane illa wani mutum da ke mutunta manya. Shugaban ƙasa ya kira kowane ɓangare kuma ya zo da yarjejeniyar da za mu aiwatar."
"Wannan yarjejeniya da kuke ganin ina bi sau da ƙafa ba umarnin kundin tsarin mulki bane, maslaha ce ta siyasa da nufin warware matsala kuma ina haka ne saboda mutunta shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

"Amma, bari na faɗa maku, idan wannan matakin da na yarda da shi ana ganin kamar wani rauni ne, to zan ba su mamaki. Ina son wannan sakon ya shiga kunnuwansu.”

Legit Hausa ta rahoto cewa jihar Ribas na fama da rikicin siyasa wanda ya ɓarke tun a watan Oktoba, 2023 sakamakon yunƙurin majalisar dokoki na tsige Fubara.

Kwamitin binciken Shaibu ya fara zama

A wani rahoton kuma Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, na tsaka mai wuya yayin da kwamitin da aka kafa ya fara zama ranar Laraba.

Tun farko babban alkalin jihar Edo ya kafa kwamitim mutum bakwai da zai binciki zargin da ake wa Shaibu wanda ya jawo majalisa ke shirin tsige shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel