Bayan Kaduna, Gwamnan APC Ya Zargi Uban Gidansa da Yashe Lalitar Gwamnati Gaba Ɗaya

Bayan Kaduna, Gwamnan APC Ya Zargi Uban Gidansa da Yashe Lalitar Gwamnati Gaba Ɗaya

  • Gwamnatin jihar Kuros Riba ta koka kan yadda ta tsinci kanta a matsanancin rashin kuɗi domin gudanar da ayyuka
  • Gwamnatin ta zargi tsohon gwamnan jihar, Ben Ayade da yashe lalitar gwamnati da kuma barin matattun ayyuka
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya koka da tulin bashi da Nasir El-Rufai ya bar masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kuros Riba - Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya bayyana yadda ya samu lalitar gwamnatin jihar.

Otu ta zargin uban gidansa, Ben Ayade wanda shi ma ɗan APC ne da yashe lalitar gwamnatin jihar kafin barin ofis.

Kamar na Kaduna, Gwamna APC ya zargi gwamnatin baya da lalata komai a jiharsa
Gwamnan Kuros Ribas ya zargi uban gidansa da bar masa tulin bashi kamr na jihar Kaduna. Hoto: Bassey Otu.
Asali: Twitter

Halin da gwamnan ya tsinci jihar ciki

Kara karanta wannan

Lamunin karatu: Tsare-tsaren da gwamnati ta yi na fara ba dalibai rancen kudi

Gwamna Otu ya ce lokacin da ya karbi ragamar mulkin jihar, bai samu komai a asusun ba sai lalatattun ayyuka a jihar, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishina ayyuka a jihar, Ankpo Edet shi ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Calabar da ke jihar.

Sai dai Edet ya ce duk da matsalar kudin, Gwamna Otu ya yi ayyukan raya kasa a birnin Calabar da keyawe, a cewar The Nation.

Ayyukan da gwamnan ke yi duk da bashin

Ya ce sun samar da sabbin hanyoyi tare da gyara wadanda suka lalace inda ya ce nan ba da jimawa ba za a sake kirkirar wasu sabbin a jihar.

"Irin lalatattun ayyuka da muka samu ya ba ni tsoro a matsayina na kwamishina inda na shiga rudani yayin da na zagaya cikin birnin Calabar."

Kara karanta wannan

Bashin Kaduna: Shehu Sani ya ba Uba Sani shawarar matakin da zai dauka kan El-Rufai

"Duk da haka mun yi abin a zo a gani duk da rashin kuɗi da muke fuskanta a wannan gwamnati ta Bassey Otu."

- Ankpo Edet

Uba Sani ya koka da tulin bashi

A baya, mun baku labarin cewa, Gwamna Uba Sani ya koka kan yadda tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya karbo bashi.

Gwamnan ya bayyana haka yayin wani taro a birnin Kaduna inda ya ce bashin ya yi yawa yadda ba su iya aiwatar da wasu ayyuka.

Sani ya ce bashin na cinye mafi yawan kuɗin da suke karba daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi da sauran harkoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel