Zai Yi Wahala APC Ta Kai Labari, Jiga-jigan Jam'iyya Sun Gargadi Tinubu Kan Halayen Ministansa

Zai Yi Wahala APC Ta Kai Labari, Jiga-jigan Jam'iyya Sun Gargadi Tinubu Kan Halayen Ministansa

  • Jiga-jigan jam'iyyar APC a birnin Tarayya, Abuja sun yi barazana ga Shugaba Bola Tinubu kan zabe mai zuwa na 2027
  • Shugabannin jam'iyyar sun bukaci Tinubu ya ja kunnen Ministan Abuja, Nyesom Wike kan nuna wariya a mukamai
  • Har ila yau, sun zargi Wike da fatali da 'ya'yan jam'iyyar da fifita 'yan jami'yyarsa ta PDP mai hamayya a mukamai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugabanninta jam'iyyar APC a Abuja sun yi Allah wadai da mukaman da Nyesom Wike ya nada.

Shugabannin suka ce Wike ya na kokarin cusa 'yan jami'yyarsa ta PDP a mukaman a madadinsu, cewar Thisday.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan takara a PDP ya gwangwaje shugabannin jam’iyyar da N7.8m

APC ta yi gargadi ga Tinubu kan halayen Wike a Abuja
APC ta bukaci Tinubu ya gargadi Wike ka da ya jawo rashin nasara ga jami'yyar a zabe. Hoto: Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Menene APC ke kira ga Tinubu kan Wike?

Jiga-jigan jami'yyar sun bayyana haka ne a Abuja yayin ganawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar 'yan jaridu (NUJ).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bukaci Shugaba Tinubu ya gargadi Wike kafin ya lalata jam'iyyar a birnin Abuja musamman kan zaben 2027.

Jigon jami'yyar a Abuja, Abdulwahab Ekekhide shi ya bayyana haka inda ya ce an yi fatali da mambobin jami'yyar a birnin, cewar Leadership.

"Muna kira ga Shugaba Tinubu da ya gargadi Wike kan irin mukamai da ya ke naɗawa a birnin Abuja."
"Dole ya rinƙa ba 'yan jam'iyyar dama idan ba haka ba APC za ta iya rasa kason da ake bukata a zaben 2027."

- Abdulwahab Ekekhide

Dalilin gargadin APC ga Tinubu kan Wike

Wannan na zuwa ne bayan Wike ya nada Hon. Chidi Amadi a matsayin shugaban ma'aikatansa, cewar Liberty Radio.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya bayyana ɗan takarar da zai lashe zaben gwamnan jihar Edo a 2024

Har ila yau, Shugaba Tinubu ya nada Hon. Felix Amaechi a matsayin kwadinetan hukumar gudanarwa ta birnin Abuja.

Wadannan nade-nade sun jawo cece-kuce musamman a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC da suka sha wahala wurin kawo gwamnatin Tinubu.

Wike ya gargadi makiyaya

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tura sakon gargadi ga makiyaya a birnin Abuja.

Wike ya ce ba zai lamunci yadda makiyaya ke kiwo kara zube a tsakiyar birnin ba wanda ke jawo matsaloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel