Fulani: Ministan Tinubu Ya Fadi Matakin da Zai Dauka Kan Makiyaya da Ke Kiwo Barkatai a Abuja

Fulani: Ministan Tinubu Ya Fadi Matakin da Zai Dauka Kan Makiyaya da Ke Kiwo Barkatai a Abuja

  • Yayin da ake fama da matsalar tsaro a Abuja, Ministan Nyesom Wike ya yi magana kan Fulani makiyaya da ke kiwo a tsakiyar birnin
  • Wike ya ce za su dauki matakin dakile matsalar kiwace-kiwace da shanu musamman a cikin birnin wanda ke addabar mutane
  • Ministan ya bayyana haka a yau Laraba 6 ga watan Maris a Abuja yayin ganawa da jakadan kasar Belgium, Daniel Bertrand

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya nuna damuwa kan yadda makiaya ke yawo a tsakiyar birnin Abuja.

Wike ya ce akwai tsare-tsare a kasa da za su tabbatar da hana makiyayan yawo barkatai da shanun a cikin birnin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya amince a gaggauta raba wa mazauna Abuja kayan abinci

Minista ya sha akwashin dakile matsalar da Fulani ke jawo wa a Abuja
Wike ya sha alwashin hana kiwo barkatai a birnin Abuja. Hoto: Fulani Connect, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Wane gargadi Wike ya yi kan Fulani?

Ministan ya bayyana haka a yau Laraba 6 ga watan Maris yayin ganawa da jakadan Belgium, Daniel Bertrand, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya gana da masu ruwa da tsaki da dama kan wannan matsalar domin ganin an hana hakan musamman a cikin birnin.

Ya kuma ce yaki da ta’addanci ya na bukatar hadin kan bangarori da dama wanda yanzu haka gwamnatin tarayya ke kokarin yi.

Matsalar tsaro a birnin Abuja

A martaninsa, Bertrand ya nuna damuwa kan yadda makiyayan ke yawo kara zube musamman a cikin birnin, cewar Daily Post.

Jakadan ya nuna jin dadinsa ganin yadda ministan ya tsara daukar mataki domin dakile matsalar da ke damun jama'a.

Wannan na zuwa ne yayin da birnin ke fuskantar matsalar tsaro da ta shafi garkuwa da mutane da karbar kudin fansa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Fitaccen basarake ya tura sako ga Tinubu kan kafa hukumar kayyade farashi

A kwanakin baya, rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar cafke kasurguman ‘yan bindiga biyu a birnin da suka addabe ta.

An shawarci Tinubu kan tsadar rayuwa

Kun ji cewa Oba na Iwoland, Oba Abdulrosheed Akanbi ya bai wa Shugaba Tinubu shawara kan tsadar kayayyaki.

Akanbi ya ce ya kamata Tinubu ya kafa hukumar kayyade kayayyakin masarufi domin dakile matsalar da ake ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da matsalar tsadar kayayyaki wanda ya birkita ‘yan kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel