Jam’iyyar APC Ta Shiga Rudani Bayan Sanar Da ’Yan Takara 2 a Zaben Fidda Gwani, Bayanai Sun Fito

Jam’iyyar APC Ta Shiga Rudani Bayan Sanar Da ’Yan Takara 2 a Zaben Fidda Gwani, Bayanai Sun Fito

  • Rikita-rikita yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da ‘yan takarar gwamnan jihar Edo har mutum biyu a zaben fidda gwani
  • Wannan na zuwa bayan an sake sanar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben
  • Hakan ya biyo bayan sanar da Dennis Idahosa da shugaban kwamitin zaben, Hope Uzodinma ya yi a yau Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo – An samu matsala yayin da wani dan takarar APC ya sake nasara bayan sanar da na farko a zaben fidda gwani a jihar Edo.

Wannan na zuwa bayan an sake sanar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

APC ta sanar da dan takararta na gwamna a zaben fidda gwani da aka gudanar, bayanai sun fito

'Yan takarar jamiyyar APC 2 sun yi nasara a zaben fidda gwani
An samu hargitsi bayan APC ta sanar da 'yan takarar gwamna 2. Hoto: Hon. Dennis Idahosa, Good Governance Movement.
Asali: Facebook

Mene ya jawo sake sanar da dan takara?

Hakan ya biyo bayan sanar da Dennis Idahosa da shugaban kwamitin zaben, Gwamna Hope Uzodinma ya yi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta tattaro cewa jam’iyyar APC a jihar ce ta sanar da Okpebholo a zaben da aka yi yau Asabar 17 ga watan Faburairu.

Ogbuaja Stanley wanda ya sanar da Okpebholo ya yi fatali da hukuncin Hope Uzodinma da ya sanar da Idahosa a matsayin dan takara.

Stanley bayan fatali da sanarwar Uzodinma ya ce mukamin da aka bai wa gwamnan Imo kawai suna ne ba shi da tasiri.

Martanin APC kan zaben a Edo

Har ila yau, zaben fidda gwanin da aka gudanar karkashin Uzodinma ya ci karo da matsaloli bayan ‘yan daba sun hargitsa zaben.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna a APC ya sake janye takara ana daf da zabe, ya fadawa Ganduje dalilansa

Uzodinma daga bisani ya ce an samu matsala dangane da wurin gudanar da zaben amma sanarwar da ya yi ta na kan hanya.

Bayan samun ‘yan takarar guda biyu APC ta yi magana kan lamarin inda ta ce Uzodinma shi ke kan dai-dai, cewar The Nation.

Kakakin jam’iyyar, Felix Morka ya ce:

“Muna sanar da ku cewa kwamitin zabe karkashin Hope Uzodinam shi ne halastacce da zai dauki matakin karshe kan zaben fidda gwani a jihar Edo.”

Idahosa ya samu nasara

Kun ji cewa, dan Majalisar Tarayya a jihar Edo, Dennis Idahosa ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani a APC.

Idahosa ya samu nasarar ce bayan zaben fidda gwani da aka yi na jam’iyyar APC a yau Asabar 17 ga watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel