Rikici Ya Shigowa ‘Yan Jam’iyyar APC, An Aikawa Shugaban Kasa Korafin Gwamna

Rikici Ya Shigowa ‘Yan Jam’iyyar APC, An Aikawa Shugaban Kasa Korafin Gwamna

  • ‘Yan majalisar tarayya daga jihar Ondo sun rubuta wasikar gabatar da korafinsu zuwa ga Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Jagororin na APC sun zargi Gwamna Lucky Aiyedatiwa da kawo tarnaki bayan karbar mulki a hannun Rotimi Akeredolu
  • ‘Yan siyasar sun fadawa shugaban kasa cewa ana watsi da shugabannin jam’iyyar APC a gwamnatin Aiyedatiwa a Ondo

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ondo - ‘Yan majalisar da ke wakiltar mazabun jihar Ondo a majalisar tarayya a karkashin APC suna da korafi a jam’iyya mai mulki.

Premium Times ta ce ‘yan majalisar sun aika budaddiyar wasika ga shugaba Bola Tinubu suna kuka da gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Lucky Aiyedatiwa
'Yan APC sun kai karar Lucky Aiyedatiwa ga Bola Tinubu Hoto: @LuckyAiyedatiwa, @Dolusegun16
Asali: Twitter

‘Ya ‘yan na APC suna zargin cewa tun da aka rantsar da sabon gwamna bayan mutuwar Oluwarotimi Akeredolu, abubuwa suka cabe.

Kara karanta wannan

Ribadu: Bayanai sun fito bayan kus-kus da Hadimin Tinubu yayi da Sanatoci a Majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar ta zargi Mai girma Lucky Aiyedatiwa da nuna kiyayya ga Marigayi Rotimi Akeredolu.

'Yan majalisar APC sun kai korafi

‘Yan majalisar da suka sa hannu a takardar su ne Adesida Abiodun Cornelius, Timehin Adelegbe Festus Ayodele sai Ojogo Donald.

Sannan akwai Odimayo Okunjimi da Adegboyega Adefarati masu wakiltar Akure, Akoko, Okitipupa, Irele, Ileoluji-Okeigbo da Odigbo.

Adesida Abiodun ya ce dalilin jan hankalin shugaban kasa shi ne saboda ya dauki mataki a kan rikcin da wuri tun kafin zaben 2024.

‘Dan majalisar yake cewa muddin ba ta canza zani ba, APC za ta iya rasa mulkin Ondo.

Laifin da gwamna ya yi wa APC a Ondo

Wasikar ta zargi sabon gwamnan da hada-kai da ‘yan adawan APC da makiyan magabacinsa tun da aka rantsar da shi a Disamba.

Wasikar ta bada misali da Kola Olawoye wanda aka nada a matsayin shugaban yakin neman zabe duk da an dakatar da shi daga APC.

Kara karanta wannan

Yaron Sarki ya ci zaben Majalisar Tarayya, zai zama ‘dan autan majalisa a shekara 32

Tsohon Kwamishinan shari'ar ya samu matsala da gwamnati da shugabannin APC na jihar. Jaridar Leadership ta fitar da wannan rahoto.

Masu korafin sun ce an yi watsi da Ade Adetimehin wanda shi ne shugaban APC, an hada kai da sanannun ‘yan adawar jam’iyya mai-ci.

Rahoton ya ce ‘yan majalisar sun zargi gwamnan da jero ayyukan marigayi Akeredolu a matsayin ayyukan da gwamnatinsa tayi.

An zargi gwamnatin APC da facaka a Ondo

Duk da ana kiran babu-babu kudi, ana da labari yadda Rotimi Akeredolu ya ba tsofaffin Gwamnoni da Mataimakansu N10bn.

Shugabannin da suka yi mulki a Jihar Ondo zasu lamushe 5.7% daga cikin kasafin kudin 2021, wasu sun soki wannan matsaya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel