‘Dan Siyasa Ya Hakura da Kujera, Saboda Magudi Aka Shirya Domin Ya Lashe Zaben Majalisa

‘Dan Siyasa Ya Hakura da Kujera, Saboda Magudi Aka Shirya Domin Ya Lashe Zaben Majalisa

  • Da aka shirya zaben ‘yan majalisa a kasar Fakistan, Hafiz Naeem Ur Rehman yana cikin wadanda aka sanar da nasararsu
  • ‘Dan takaran ya fito yana shaidawa duniya cewa ba zai karbi kujerar siyasa ba, dalilinsa kuwa shi ne an shirya magudin zabe
  • Saboda a ba shi nasara a zaben da aka yi, Hafiz Naeem Ur Rehman ya ce an murde dubban kuri’un da aka ba abokin adawarsa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Fakistan - Hafiz Naeem Ur Rehman da aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben lardin Karachi a kasar Fakistan ya fasa rike mukamin.

Rahoton BBC ya ce Hafiz Naeem Ur Rehman ya ki amincewa ya dare kujerar majalisa bayan an sanar da ya yi nasara a zaben da aka shirya.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda Gwamnatin Buhari ta ‘saida’ man shekaru masu zuwa

'Dan siyasa
'Dan siyasa a Fakistan, Hafiz Naeem Ur Rehman Hoto:www.geo.tv
Asali: UGC

Magudi ko zaben halal a Fakista?

Hafiz Naeem Ur Rehman wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar Jamaat-e-Islami yana zargin cewa an yi magudi ne domin ya yi nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar yana ganin da murdiyar ne ya iya doke babban abokin hamayyarsa, Saif Bari wanda ya tsaya ba karkashin wat jam’iyya ba.

Dokar Fakistan ta halatta shiga zabe a matsayin ‘dan takara mai cin gashin kai, a haka mutanen Imran Khan suka yi nasara a zabukan.

'Yan Tehreek-e-Insaf (PTI) sun sake takara

An hana jam’iyyar tsohon Firayim Minista Imran Khan watau Tehreek-e-Insaf (PTI) tsaida ‘yan takara a zaben da aka shirya na Fubrairu.

Rehman aka sanar a matsayin wanda ya yi galaba a mazabar PS – 129, tashar NBC ta ce ‘dan takaran ya tashi da kuri’u har fiye da 26, 000.

Kara karanta wannan

Yaron Sarki ya ci zaben Majalisar Tarayya, zai zama ‘dan autan majalisa a shekara 32

Ana haka sai aka ji ‘dan takaran yana mai cewa an rage kuri’un Bari daga 31, 000 zuwa 11, 000 bayan dubban Bayin Allah sun zabe shi.

Saboda murdiyar da aka yi wa abokin gwabzawarsa, Rehman ya ce ba zai karbi nasarar da aka ba shi a takarar wannan shekarar ba.

Jawabin Naeem Ur Rehman bayan 'nasarar' zabe

"Idan wani yana so mu yi nasara ta hanyar da ba ta halatta ba, ba za mu amince da wannan ba”
"Dole a girmama ra’ayin al’umma. A bar wanda ya yi nasara ya yi nasara; a bar wanda ya fi ya fadi."

- Hafiz Naeem Ur Rehman

Wanene zai zama 'dan majalisar Kurachi?

Reuters ta rahoto wannan ‘dan siyasa yana cewa bai dace a yi wa wani alfarmar haram ba.

Zuwa yanzu hukumar zabe ta kasar Fakistan ba ta fadi wanda zai wakilci mutanen Karachi a majalisar tarayya bayan matakin da ya dauka ba.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya tona abin da ya jawo Wike ya goyi bayan Tinubu a kan Atiku a 2023

Hadamar 'yan siyasar Edo

A zaben tsaida gwani na biyu da NWC ta shirya a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje, ana da labari APC ta shiga rudani a jihar Edo.

Ana neman rasa gane wanene halataccen 'dan takaran APC a zaben Edo tsakanin Dennis Idahosa, Monday Okpebholo da Anamero Dekeri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel