Sanatan APC Ya Shiga Uku Yayin da Ya Ke Fuskantar Shari’a Kan Kalamansa, an Ba Shi Zabi

Sanatan APC Ya Shiga Uku Yayin da Ya Ke Fuskantar Shari’a Kan Kalamansa, an Ba Shi Zabi

  • Sanata Abbo na fuskantar shari’a bayan zarge-zargen cin hanci da ya yi kan alkalan Kotun Daukaka Kara
  • Elisha ya zargi Mai Shari’a, Monica Dongban-Mensem da karbar cin hanci yayin yanke huknce-hukuncen zabe
  • Wannan na zuwa ne bayan sanatan ya rasa kujerarsa yayin da alkalan Kotun Daukaka Kara suka yi hukunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo na fuskantar barazanar zuwa gidan yari kan zargin shugabar Kotun Daukaka Kara.

Elisha ya zargi Mai Shari’a, Monica Dongban-Mensem da karbar cin hanci yayin yanke huknce-hukuncen shari’ar zabe.

Sanatan APC na fuskantar shari'a kan kalamansa
An bukaci Sanata Abbo ya ba da hauri kan kalamansa ko ya fuskanci shari'a. Hoto: Elisha Abbo.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Abbo da aikatawa?

Rahotanni sun tattaro cewa Monica ta bai wa Sanatan wa’adi don tabbatar da zarginsa ko kuma fuskantar shari’a.

Kara karanta wannan

APC tayi maganar yunkurin dawo da Sanusi II gidan sarauta da rushe masarautun Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Monica ta bukaci ya nemo hujjoji don kare zargin da ya ke yi ko ya fuskanci barzanar shari’a kan abubuwan da ya fada ba tare da hujja ba.

Ta kuma bukace shi da ya bai wa Mai Shari’a, Chioma Iheme hakuri da kuma bangaren shari’ar kasar kan zarge-zargen, cewar Channels TV.

Babban lauya kuma tsohon kwamishinan shari’a a jihar Akwa Ibom, Uwemedimo Nwoko ya ce dole Abbo zai fuskanci shari’a don nemo hujjoji ko ya ba da hakuri.

Nwoko ya ce tabbatar da abin da ya ke zargin shi ne kawo hujjoji da za su kare zarge-zargen da ya ke yi kan bangaren shari’a, cewar The Guardian.

Wane shawara aka bai wa Abbo?

Nwoko ya ce:

“Wannan shirme da ake yi wurin cin mutunci da cin zarafin bangaren shari’a dole a kawo karshenshi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

“Ina kalubalantar Sanata Abbo da ya kawo hujjoji da za su kare zarge-zargen da ya ke yi ko kuma ya fuskanci shari’a.”

Wannan na zuwa ne bayan sanatan a ranar 1 ga watan Faburairu ya zargi Shugaban Kotun Daukaka Kara kan zargin karbar rashawa.

Abbo ya zargi bangaren shari’a da rashawa

Kun ji cewa sanata Elisha Abbo ya zargi bangaren shari’a da karbar cin hanci da rashawa a kararrakin zaben da aka gudanar.

Abbo wanda tsohon sanata ne da ya wakilci Adamawa ta Arewa na zargin alkalan Kotun Daukaka Kara da karbar na goro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel