APC Tayi Maganar Yunkurin Dawo da Sanusi II Gidan Sarauta da Rushe Masarautun Kano

APC Tayi Maganar Yunkurin Dawo da Sanusi II Gidan Sarauta da Rushe Masarautun Kano

  • Jam’iyyar APC ba ta goyon bayan kiraye-kirayen da aka fara na dawo da Muhammadu Sanusi II
  • Ahmad Aruwa ya yi wa ‘Yan Dangwalen Jihar Kano raddi bayan sun aikawa majalisar Kano takarda
  • Kakakin APC na reshen Kano ya zargi gwamatin NNPP ta fakewa da wasu domin taba Sarakunan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Wata kungiya ta ‘Yan Dangwalen Jihar Kano ta tada kura da ta aikawa majalisar dokoki takarda game da masarautu.

Punch ta ce jam’iyyar APC ta gargadi majalisa game da wannan shiri, ta ce yin hakan ba zai jawo komai ba illa tashin-tashina a Kano.

Sanusi II
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II Hoto: @MSII_dynasty/Getty
Asali: Twitter

APC tana ganin watsi da tsarin masarautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kawo a shekarar 2019 ba zai haifar da ‘da mai ido ba.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ra’ayin Alhaji Ahmad Aruwa, kiran taba gidajen sarauta shiriritar banza ce kurum. Tun kwanaki Rabiu Kwankwaso ya dauko maganar.

Sakataren yada labaran na APC Kano ya yi watsi da batun, yana ganin babu ta yadda kungiya za ta fadawa gwamnati abin da za ta aikata.

Nasarar kirkiro sababbin Sarakuna a Kano

Ahmad Aruwa yake cewa Abdullahi Umar Ganduje ya cin ma nasarori da yawa a lokacin da ya yi mulki tsakanin Mayun 2015 da 2023.

Daga cikin nasarorin gwamnatin Ganduje akwai kirkiro sababbin masarautu da ya yi.

Sarakuna: APC tana so Abba ya daina kama-kame

Ahmad Aruwa yake cewa idan gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana so ta rusa masarautu, ta daina fakewa da kungiya, ta fito kai tsaye.

"APC a matsayin jam’iyya ba ta damu ba, domin gwamnatin jiha a karkashin tsohon gwamna Ganduje tayi abin da ya kamata,"

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

"ta hanyar kirkiro masarautu kuma mutane sun ga muhimmancinsu."
"Abin da Kano take bukata a yanzu shi ne zaman lafiya, ba abin da zai jawowa jihar da mazaunanta rigima ba."

- Ahmad Aruwa

Menene ra'ayin NNPP a kan masarautu?

Rahoton ya nuna da alama jam’iyyar NNPP ba ta kan ra’ayin da APC mai adawa ta dauka.

Da aka zanta da shugaban NNPP na reshen Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya ce kowa da ra’ayinsa, bai soki matsayar kungiyar ba.

Za a dawo da Muhammadu Sanusi II?

An ji labari ‘yan dangwale a takardar da suka aikawa ‘yan majalisa da gwamna Abba Kabir Yusuf, sun soki tsige Sanusi Lamido Sanusi.

Kungiyar ta ce Mai girma Muhammadu Sanusi II ya taimaki al’umma lokacin da yake Sarki saboda haka ta bada shawarar maido shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel