Sanatan APC Ya Roki Tinubu Ya Dakatar da Karin Girma Ga Alkaliyar da Ta Rusa Zabensa, Ya Fadi Dalili

Sanatan APC Ya Roki Tinubu Ya Dakatar da Karin Girma Ga Alkaliyar da Ta Rusa Zabensa, Ya Fadi Dalili

  • Korarren sanatan APC a jihar Adamawa, Elisha Abbo ya nemi a dakatar da rantsar da alkaliyar da ta rusa zabensa
  • Abbo wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa ya soki karin girman sa ake shirin yi wa Chioma Nwosu-Iheme zuwa Kotun Koli
  • Nwosu-Iheme na daga cikin Alkalan kotun Daukaka Kara 11 da aka tantance su a Majalisa don kara musu gurin zuwa Kotun Koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Sanata Elisha Abbo ya roki Shugaba Tinubu da ya dakatar da rantsar da alkaliyar kotun da ya rusa zabensa.

Sanatan wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa ya soki karin girman sa ake shirin yi wa Chioma Nwosu-Iheme zuwa Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano ya raba gari da Shugaba Tinubu kan tsige 'dan Arewa daga muhimmin mukami

Sanatan APC ya roki Tinubu babbar bukata bayan rusa zabensa
Sanata Abbo ya tura sako ga Shugaba Tinubu bayan rusa zabensa. Hoto: Bola Tinubu, Elisha Abbo.
Asali: Facebook

Mene dalilin Abbo kan alkaliyar?

Nwosu-Iheme na daga cikin Alkalan kotun Daukaka Kara 11 da aka tantance su a Majalisa don kara musu gurin zuwa Kotun Koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abbo ya bayyana haka ne a yau Laraba 31 ga watan Janairu yayin hira da manema labarai a Abuja, cewar TheCable.

Sanatan ya ce alkalan biyar da suka yanke hukuncin sun yi kuskuren tabbatar da Amos Yohanna na PDP a kujerar.

Ya ce ya tura takarda ga hukumar NJC da Tinubu don dakatar da karin girman har sai an gama bincike tukun.

Rokon Abbo ga Shugaba Tinubu

A cewarsa:

"Magana ta a nan ita ce nada Chioma Nwosu-Iheme zuwa Kotun Koli matsala ce ga bangaren shari'a a Najeriya."

Abbo ya kuma roki Shugaba Tinubu da ya shirya kawo sauyi a kasar wurin dakatar da karin girman gare ta don ceto bangaren shari'ar kasar.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan yarjejeniyarsu da Tinubu don komawa APC, ya yi godiya

Ya ce Kotun Daukaka Kara ta tafka kuskure yayin hukuncin inda ya ce ba ya neman a sake zama kan hukuncin, cewar The Street Journal.

Lauya ta maka Tinubu da gwamnoni 36 a kotu

Kun ji cewa wata babbar lauya a Najeriya, Funmi Falana ta maka gwamnonin jihohi 36 a kotu kan kudaden hukumar UBEC.

Har ila yau, ta maka birnin Abuja kan kin biyan wasu kudade don samun damar amfani da biliyan 68 don ba da ilimi kyauta ga dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.