Gwamnan Kaduna Ya Fadi Abu Guda 1 Tak da Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro a Arewa

Gwamnan Kaduna Ya Fadi Abu Guda 1 Tak da Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro a Arewa

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya magantu kan matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Yammacin kasar
  • Sanata Uba Sani ya ce sai an magance matsalolin rashin aikin yi da talauci idan har ana so a cimma nasara a yaki da ta'addanci
  • Ya kuma ce hakan ba zai yiwu ba har sai an samu shugabanci na gari wanda da shi za a warware wadancan matsalolin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa talauci da rashin aikin yi ne suka haddasa matsalolin tsaro na ‘yan fashi da sace-sacen jama’a a yankin Arewa maso Yammacin kasar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa hanya mafi dacewa da za a bi wajen shawo kan matsalar ita ce wanzar da shugabanci na gari, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Uba Sani ya ce sai da shugabanci na gari za kawo karshen rashin tsaro
Gwamnan Kaduna Ya Fadi Abu Guda 1 Tak da Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro a Arewa Hoto Uba Sani
Asali: Twitter

Uba Sani ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin Kaduna a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu, yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar dattawan Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattawan sun kai masa ziyara ne don taya shi murnar nasarar da ya samu a Kotun Koli.

Ya ce gwamnatin jihar Kaduna na kara kaimi wajen yaki da ‘yan fashi da garkuwa da mutane tare da goyon bayan hedkwatar tsaro, wacce za ta gina karin sansanin soji guda biyu a jihar, rahoton The Cable.

Haka kuma, Gwamna Sani ya ce gwamnatinsa tana daukar kyakkyawan shugabanci a matsayin hanya mafi dacewa wajen magance matsalolin tsaro.

Hanyoyin samun zaman lafiya a Arewa

Gwamna Sani, ya kuma ce dole a magance matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta domin tabbatar da tsaro a jiha da yanki.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tono tushen matsalar ƴan bindiga a Arewa, ya jero hanyoyin magance su

Ya kuma bayyana cewa jihar na samun tallafin dala miliyan 28 daga kasar Kuwait domin magance matsalar yaran da ba su zuwa makaranta.

"Babban hanyar samun maslaha shine shugabanci nagari. Duk yadda muka kai ga magana da kokarin kawo zaman lafiya, ida ba mu dba bangaren shugabanci nagari ba, ba za mu taba kawo karshen matsalar rashin tsaro ba musamman a Arewacin Najeriya."

Kotu ta umurci Tinubu ya kayyade farashin kaya

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya dake zama a Ikoyi, Legas ta umurci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyaki da man fetur cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a Ambose Lewis-Allagoa ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, a wata kara da 'dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya shigar, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel