Tsadar Rayuwa: Jigon APC Ya Gaji da Tsarin Tinubu, Ya Nemi a Sake Zama Kan Tsare-tsaren Gwamnati

Tsadar Rayuwa: Jigon APC Ya Gaji da Tsarin Tinubu, Ya Nemi a Sake Zama Kan Tsare-tsaren Gwamnati

  • Jigon jami'yyar APC a Najeriya, Salihu Lukman ya caccaki jami'yyar yayin da jama'ar kasar ke cikin wani mawuyacin hali
  • Salihu ya ce a yanzu kokarin sabunta burin 'yan Najeriya da Tinubu ke yi, ya sabunta kunci ne kawai a rayuwarsu
  • Lukman ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Abuja inda ya bukaci gwamnati ta yi wani abu kan wahalalun da ake ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma ya caccaki jami'yyar kan halin da ake ciki.

Salihu Lukman ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Abuja inda ya bukaci gwamnati ta yi wani abu kan wahalalun da ake ciki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya fadi hanya 1 tak da Najeriya za ta samu ci gaba mai dorewa

Jigon APC ya caccaki Tinubu kan wahalar da ake sha a Najeriya
Jigon APC, Salihu Lukman ya soki tsarin Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, Salihu Lukman.
Asali: Facebook

Mene jigon APC ke cewa kan Tinubu?

Lukman ya ce tsare-tsaren Shugaba Tinubu na sabunta burin 'yan Najeriya ya sabunta musu bakin ciki ne a kasar, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta yi katutu wanda har ya jawo barkewar zanga-zanga a biranen Minna da kuma Kano a ranar Litinin.

Ya kara da cewa wannan duk ya na faruwa ne kasa da shekara daya na mulkin Shugaba Tinubu kan karagar mulkin Najeriya.

Salihu ya bukaci saukin gaggawa a kasar musamman tsadar kayan abinci a kasar da kullum ke tashin gwauron zabi, cewar Independent.

Shawarin Jigon APC ga Tinubu

A cewarsa:

"Akwai munanan labarai daga 'yan Najeriya da ke zuwa kasuwanni wanda farashin ke sauyawa kasa da awanni 24.
"Dukkan wadannan abubuwa na faruwa ne saboda tsare-tsaren da Shugaba Tinubu ke dauka a fannin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Mahara sun sake hallaka fitaccen basarake a jihar Arewa, bayanai sun fito

"Zanga-zangar Minna da Kano ya tabbatar da abin da nake fada a baya cewa akwai matsala idan har ba a dauki matakai ba."

APC ta zargi jam'iyyun adawa kan zanga-zanga

Kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta zargi jam'iyyun adawa da daukar nauyin zanga-zanga da ake yi a kasar.

Jami'yyar ta ce ya kamata sun kawo mafita ne ga matsalar da ake ciki ba wai kushe tsare-tsaren gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel