Ana Son Kifar da Tinubu, APC Ta Tona Asirin Wadanda Suka Dauki Nauyin Zanga-zanga a Kano da Neja

Ana Son Kifar da Tinubu, APC Ta Tona Asirin Wadanda Suka Dauki Nauyin Zanga-zanga a Kano da Neja

  • Jami'yyar APC ta nuna damuwa kan yadda ake daukar nauyin masu zanga-zang a fadin kasar baki daya
  • Jami'yyar ta ce rashin kishin kasa ne yadda ake neman bata wa gwamnatin Bola Tinubu suna
  • Sakataren yada labaran jami'yyar, Felix Morka shi bayyana haka a yau Talata 6 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jami'yyar APC mai mulkin Najeriya ta zargin jam'iyyun adawa da ingiza mutane don yin zanga-zanga a biranen kasar.

Jami'yyar ta ce rashin kishin kasa ne yadda ake neman bata wa gwamnatin Bola Tinubu suna don biyan bukatar kansu.

APC na zargin wasu da daukar nauyin zanga-zanga don biyan bukatar kansu
APC ta zargi jam'iyyun adawa da daukar nauyin zanga-zanga. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Wane zargi APC ke yi?

A jiya Litinin 5 ga watan Faburairu ce mata da matasa suka cika titunan birnin Minna da ke Neja don yin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zangar sun fito ne don nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake fama da tsadar rayuwa a fadin kasar baki daya.

Har ila yau, zanga-zangar ta sake barkewa a birnin Kano kan mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki, cewar Channels TV.

Sakataren yada labaran jami'yyar, Felix Morka ya ce an kirkiri zanga-zangar ce don durkusar da gwamnatin Bola Tinubu.

Martanin APC kan zanga-zangar

Ya ce:

"Zanga-zanga a biranen Minna da Kano a jiya Litinin 5 ga watan Faburairu aikin wadansu marasa kishin kasa ne.
"Faruwar zanga-zangar lokaci guda a manyan biranen biyu akwai alamun tambaya ba haka kawai ya faru ba.
"Duk da mun yi imani da yin zanga-zanga cikin lumana, amma ya kamata mutane su hankalta kada ana yin amfani da su wurin ta da zaune tsaye."

Kara karanta wannan

Za a gamu da sabon cikas wajen gine-gine, ma’aikata sun tafi yajin-aiki daga yau

Morka ya ce wannan shiri ne na jam'iyyun adawa don kawo cikas a gwamnati kuma hakan barazana ce ga zaman lafiyar kasar baki daya.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta himmatu wurin tabbatar da tsare-tsaren da za su kawo sauki ga al'umma da kuma ci gaban kasa, cewar Vanguard.

An yi zanga-zanga a Arewacin Najeriya

Kun ji cewa a jiya Litinin 5 ga watan Faburairu ce zanga-zanga ta barke a birnin Minna da ke jihar Neja.

Masu zanga-zangar sun koka kan yadda tsadar rayuwa ta hana mutane sakat da kuma rashin daukar matakai da za su saukaka hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel