Gwamnan Kano, Abba Yusuf, Ya Fadi Hanya 1 Tak da Najeriya Za Ta Samu Ci Gaba Mai Dorewa

Gwamnan Kano, Abba Yusuf, Ya Fadi Hanya 1 Tak da Najeriya Za Ta Samu Ci Gaba Mai Dorewa

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa har sai an samu hadin kai ne za a samu dawwamammen ci gaba a Najeriya
  • Yusuf ya bayyana hakan a jihar Abia, yayin da ya halarci bikin cika shekara 66 na hamshakin dan kasuwa Chief Akwukwaegbu
  • Da ya samu wakilcin mai bashi shawara ta fuskar harkokin waje, gwamnan ya ce akwai bukatar karfafa sada zumunci a tsakanin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Abia - An bukaci al'ummar Najeriya da su karfafa hadin kan da ke tsakanin su domin samar da dawamammen ci gaba a kasar.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da bukatar a bukin cika shekaru 66 na hamshakin dan kasuwa, Uche James Akwukwaegbu a jihar Umuahia.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ku yi hakuri da Tinubu, jigon APC ya roki 'yan Najeriya

Alhaji Shittu ya wakilci Gwamna Yusuf a jihar Abia
Alhaji Shittu ya wakilci Gwamna Yusuf a jihar Abia, ya nemi a hada kai don ci gaban kasa. Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Gwamnan ya buga misali da cewa ba karamin dace bane mutum ya shafe shekaru 66 cikin koshin lafiya a Najeriya, saboda tsadar rayuwa, The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karfafa zumunci ne zai kawo ci gaba a Najeriya - Yusuf

Da ya samu wakilcin Alhaji Mashood Shittu, mai bashi shawara na musamman ta fuskar harkokin waje, Yusuf ya ce har sai an karfafa sada zumunci ne za a cike gibin kaunar juna.

Ya ce:

"Na sanar da mutane daga nesa cewa Najeriya na da karfi ne saboda hadin kan 'yan kasar, kuma har sai mun karfafa zumunci ne za mu wanzar da wannan ci gaban.
"Misali akan shari'ar NNPP da aka yi a Kano, kuma duk inda na je a Abia sai in ji suna cewa NNPP a Kano take kawai, amma gashi ta karade kasar baki daya."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Dalilin da ya sa gwamna ya tura wakilci zuwa Abia

Da yake magana akan Chief Akwukwaegbu, Shittu ya ce:

"A yau na zo ne domin karfafa zumuncin da ke tsakanin mu, domin Akwukwaegbu masoyin tafiyar Kwankwasiyya ne. Kenan na zo nan ne domin na wakilcin kafatanin mabiya Kwankwasiyya.
"Muna godiya kwarai akan addu'o'in da mutanen Abia suka riƙa yi, tare da dagewa akan lallai kada a kwace Kano daga hannun NNPP saboda sun san mune muka ci zabe."

Da yake wakiltar gwamnan jihar Abia a wajen taron, kwamishinan masana'antu na jihar, Chimezie Ukaegbu, ya gwarzonta Akwukwaegbu na kasance mai kishin kasa.

Abdul Samad Rabiu ya tafka asarar dala biliyan 2.7

A wani labarin kuma, hamshakin dan kasuwar Najeriya daga jihar Kano, Abdul Samad Rabiu, ya tafka asarar dala biliyan 2.7.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Najeriya ta karya darajar Naira karo na biyu a cikin watanni 8 domin farfaɗo da tattalin arziki

Asali: Legit.ng

Online view pixel