Shari’o’in Takarar Gwamnoni 3 Mafi Zafi da Za a Kawo Karshensu Yau a Kotun Koli

Shari’o’in Takarar Gwamnoni 3 Mafi Zafi da Za a Kawo Karshensu Yau a Kotun Koli

  • Za a yanke hukunci a shari’ar zaben gwamnonin jihohin Kebbi, Nasarawa, Taraba da Sokoto a safiyar yau Juma’a
  • A yau ‘yan takara da gwamnonin Delta, Ribas, Gombe, Kaduna da Ogun za su tabbatar da makomar takararsu
  • Inyang Okoro da Kudirat Kekere-Ekun za su jagoranci hukuncin karshe da za ayi a kan takarar da aka yi a 2023

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kwanaki 7 da yanke hukuncin zaben Kano da wasu jihohi 7, kotun koli za ta raba gardama a shari'o'in Ogun, Kaduna da Taraba.

Za a yanke hukunci a karar gwamnan Kebbi, Ribas, Delta, Gombe, Nasarawa da Sokoto.

Shari'ar zaben Gwamnan Kaduna
Kotun koli za ta rufe shari'ar zaben Gwamnoni Hoto: @UbaSaniUS, @IsaAshiruKudan
Asali: Twitter

1. Kaduna: PDP v APC

Isa Ashiru Mohammed Kudan da Uba Sani duk sun daukaka kara a kotun koli domin rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

An zo wajen, Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan sahihancin nasarar gwamnonin jihohi 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan takaran na PDP a zaben jihar Kaduna ya samu kuri’u 719, 196, ya ce an sabawa ka’ida kafin APC ta tashi da kuri’unta 730, 001 a 2023.

2. Nasarawa: PDP & APC

Jama’a sun zura ido domin ganin yadda za ta kaya a shari’ar gwamnan Nasarawa musamman saboda nasarar PDP a kotun korafin zabe.

Da aka je kotun daukaka kara, alkalai sun dawo da Abdullahi Sule a kan mulki, aka rusa gaskiyar da aka ba Emmanuel David Ombugadu.

3. Ogun: PDP & APC

Oladipupo Adebutu wanda ya yi takarar gwamnan jihar Ogun a PDP ya shigar da kara mai lamba SC/CV/1223/2023 domin a tsige Dapo Abiodun.

Shari’ar Adebutu da Abiodun ta ja hankali saboda yadda takararsu tayi zafi a 2023. Gwamna Abiodun ya sha da kyar ne a hannun PDP a bara.

Kara karanta wannan

Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 sun ki taya Abba murnar galaba kan APC

Sauran hukuncin da za ayi a Kotun koli

Sauran hukuncin da ake sauraro sun hada da na Ribas, inda Tony Cole da jam’iyyarsa suke so alkalai su sauke Simi Fubara daga kan mulki.

Legit ta kawo labarin shari’ar zaben gwamnan jihar Sokoto, wani hadimin ‘dan takaran PDP ya shaida mana ana fatan cire Ahmed Aliyu.

Za a kai karar PDP a kotu

Ana da labari jagora kuma mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar a zaben 2019 yana shirin kai jam'iyyarsa ta PDP kara a kotu.

Segun Showunmi ya zargi jam’iyyarsu da sabawa doka saboda rashin yin taron NEC, idan aka cigaba da tafiya a haka, za ayi shari'a da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel