Kotun Zabe Ta Soke Nasarar Uba Sani, Isa Ashiru Ya Yi Ikirari

Kotun Zabe Ta Soke Nasarar Uba Sani, Isa Ashiru Ya Yi Ikirari

  • Ga dukkan alamu za a ci gaba da fafatawa a kan zaben gwamnan 2023 a jihar Kaduna
  • A ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, kotun zaben ta ayyana zaben gamnan jihar Kaduna a matsayin wanda bai kammalu ba
  • Isa Ashiru, dan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ne ya bayyana sakamakon kotun zaben a cikin sanarwarsa da ya wallafa a soshiyal midiya

Jihar Kaduna - Dan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Kaduna, Rt Hon Isa Ashiru, ya bayyana ainahin matsayin kotun sauraron kararrakin zaben.

Ashiry ya yi ikirarin cewa kotun zaben gwamnan jihar Kaduna ta soke nasarar zaben gwamna Uba Sani.

Isah Ashiru ya ce kotun zabe ta soke nasarar Uba Sani
Kotun Zabe Ta Soke Nasarar Uba Sani, Isa Ashiru Ya Yi Ikirari Hoto: Senator Uba Sani/Isa Ashiru Kudan
Asali: Facebook

Ya kuma ce a hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, kotun zaben ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Da yake karin haske a kan hukuncin kotun zaben, Ashiru ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kotun zaben ta raba hukuncin zuwa kashi 2:1, ta soke zaben gwamnan jihar Kaduna, ta kuma ba da umarni cewa a janye takardar shaidar cin zaben tare da gudanar da sabon zabe a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomi 4, sannan a yi la’akari da sakamakon zaben kafin a bayyana wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kaduna."

Ashiru ya nemi magoya bayansa su zama masu bin doka da oda

Ashiru ya yi godiya ga magoya bayansa da kuma al’ummar Kaduna, inda ya bukace su da su kasance masu bin doka da oda sannan su guji tashin hankali.

Ya bayyana cewa zai tsaya tsayin daka a kokarinsa na kwato kuri'unsa har sai ya ga abun da ya turwa buzu nadi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Lagas: Jandor Da PDP Sun Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Zabe, Sun Bayyana Mataki Na Gaba Da Za Su Dauka

Dan takarar na PDP ya bayyana cewa:

“Ina kara mika godiyata ga al’ummar jihar tare da kira gare su da su ci gaba da bin doka da oda yayin da muke ci gaba da daukaka kara.
“Abu daya da zan tabbatar wa mutanen jihar Kaduna masu karamci shine cewa, zan bi wannan kuri'u da kuka ba ni har zuwa karshe, kuma da yardar Allah, nasara na gare mu."

Gwamna Uba Sani ya ce shi ya yi nasara a kotun zaben gwamnan Kaduna

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Uba Sani ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook inda yake tabbatar da nasararsa a kotun zaben.

Sani ya ce:

“Na yi matukar farin ciki da kuma kankan da kai ga hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da nasarar da na samu a zaben Gwamnan Jihar Kaduna a 2023.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin Labour Party Da APC Kan Kujerar Dan Majalisa

“Hukuncin ya tabbatar da yawan kuri’un da mutanen jihar Kaduna masu karamci suka bani.
“Na yaba wa kotun kan tsayin dakan da suka nuna. Sun inganta bangaren shari'armu da tsarin dimokuradiyyar zabe."

Kotun zabe ta kwace kujerar dan majalisar PDP a jihar Filato, ta bai wa APC

A wani labarin, mun ji cewa kotun saurararon ƙorafe-ƙorafen zaben 'yan majalisar jiha da na tarayya ta soke nasarar ɗan majalisar jihar Filato, Timothy Dantong, na jam'iyyar PDP.

Bayan haka Kotun ta ayyana Moses Dachum na jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Riyom a majalisar dokokin jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel