An Zo Wajen, Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnonin Jihohi 5

An Zo Wajen, Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnonin Jihohi 5

  • Kotun ƙoli ta zaɓi ranar da zata yanke hukunci kan kararrakin da aka kalubalanci nasarar gwamnonin jihohi biyar
  • A wata takarda da ta fita yau Alhamis, kotun zata sanar da hukunci kan shari'oin jihohin gobe Jumu'a, 19 ga watan Janairu
  • Jihohin da za a karkare shari'arsu sun haɗa da Ogun, Delta, Nasarawa, Gombe da kuma jihar Kebbi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin kasar nan ta sanya ranar Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar.

Jihohin da kotun zata yanke hukunci kan kararrakinsu idan Allah ya kaimu gobe sun haɗa da Ogun, Kebbi, Nasarawa, Gombe da kuma Delta, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta ɗauki mataki kan ƙarar da aka nemi tsige gwamnan APC na arewa, PDP ta hango nasara

Kotun koli ta sa ranar yanke hukunci.
Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Kararrakin Zaben Jihohi 5 Hoto: Supreme Court Of Nigeria
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a tsare-tsaren ayyukan da kotun zata yi wanda ya fito yau Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shari'ar zaben Ogun

Kotun za ta yanke hukunci kan kararraki biyu da suka shafi Ogun, masu lamba SC/CV/1221/2023 na Oladipupo Adebutu, ɗan takarar PDP da SC/CV/1223/2023 da Gwamna Abiodun na APC ya shigar.

A ƙarar da suka ɗaukaka zuwa gaban kotun ƙoli, Adebutu da PDP sun nemi a soke nasarar Abiodun.

Shari'ar zaben Gombe

A bangaren Gombe, kotun na shirin yanke hukunci kan karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Jibrin Barde, ya shigar yana neman tsige Inuwa Yahaya na APC.

Karar zaben Delta

A shari'ar Delta, kotun na shirin yanke hukunci kan kararraki uku, wanda dan takarar jam’iyyar APC, Ovie Omo-Agege ya shigar.

Dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Kenneth Gbagi da kuma Kennedy Pela na Labour Party ne suka shigar da ragowar ƙararrakin biyu.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci kan sahihancin nasarar gwamnan arewa, APC na tsaka mai wuya

Taƙaddamar zaben Nasarawa

Dangane da Nasarawa, kotun kolin za ta yanke hukunci kan kararraki hudu da dan takarar jam'iyyar PDP, Emmanuel David Ombugadu ya shigar.

Jihar Kebbi

A batun Kebbi kuma kotun mai daraja ta ɗaya zata yanke hukunci kan ƙararraki uku. Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Aminu Bande ne ya shigar da guda ɗaya.

Gwamna mai ci, Nasir Idris na APC ya shigar da ƙara ɗaya yayin da mataimakin gwamna, Abubakar Umar Argungu, ya miƙa ragowar ta ukun.

Tinubu ya gana da malamai a Villa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya sa labule da manyan malaman addinin musulunci a fadar gwamnati Aso Villa da ke Abuja yau Alhamis.

Wannan zama ya zo kwana biyu bayan shugaban majalisar shari'ar musulunci a Najeriya ya yi nadamar goyon bayan Muslim-Muslim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel