Kwanaki 5 Da Hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 Sun Ki Taya Abba Murnar Galaba Kan APC

Kwanaki 5 Da Hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 Sun Ki Taya Abba Murnar Galaba Kan APC

  • Mai girma gwamnan jihar Kano ya doke Nasiru Yusuf Gawuna a shari’ar zaben 2023 da aka gama a kotun koli
  • Sarakunan Bichi, Gaya, Karaye da Rano da aka kirkiro a shekarar 2019 sun yi tsit game da nasarar NNPP mai-ci
  • Mai martaba Aminu Ado Bayero ne ya fara fitar da sakon taya Abba murna bayan tsawon kwana da kwanaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Kwanaki biyar kenan da kotun koli ta tabbatar da Mai girma Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

Har zuwa safiyar Laraba da ake tattara rahoton nan, Sarakunan jihar Kano ba su fito sun taya gwamna Abba Kabir Yusuf murna ba.

Sarkin Kano
Sarkin Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

Hukuncin ya kawo karshen doguwar shari’ar zabe da gwamnan ya yi da APC wanda ta tsaida Nasiru Yusuf Gawuna a takarar 2023.

Kara karanta wannan

Mutane 6 da Suka Taimakawa Abba Kabir Yusuf Wajen Samun Nasarar Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a daga wurare dabam-dabam sun aiko da sakon taya murna ga Abba Yusuf.

A cikin wadanda suka aika da sakon farin ciki zuwa ga gwamnan har da jagororin PDP kamar Atiku Abubakar da Bukola Saraki.

Abba: Sarakuna sun yi shiru a Kano

Sarakunan da ake da su wadanda gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira, ba suyi wani jawabi kamar yadda aka sa rai ba.

A matsayinsu na iyayen kasa, ba a ji sun taya gwamna murna ko kira ga APC da ‘dan takaranta, Nasiru Gawuna su dauki kaddara ba.

...Sakon Sarkin Misau daga Bauchi

Salisu Hotoro wanda yake taimakawa Abba Kabir Yusuf a kafafen zamani ya yi ikirarin Masarautar Misau ta taya mai gidansa murna.

Kamar yadda ya fitar da takarda a Facebook, Hotoro ya ce Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman ya taya Abba murnar galaba kotu.

Kara karanta wannan

Kano: Sanusi II ya soki APC a maganar farko a fili bayan nasarar Abba a Kotun Koli

Abba ya hadu da Aminu Ado Bayero

A ranar Litinin, gwamna Abba Kabir Yusuf ya hadu da Mai martaba Aminu Ado Bayero wajen bikin tunawa da mazan jiya da aka yi.

Legit Hausa ba ta da masaniya a kan wainar da aka toya tsakanin Sarki da gwamna Abba sai dai wasu sun fara kiran canza mai martaba.

Sakon taya Gwamnan Kano murna

Daga baya sanarwa ta fito daga shafin Facebook, inda aka ji masarautar Kano ta taya Abba Yusuf murnar yin galaba a shari’ar zaben 2023.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya ce Sarki yana yi masa fatan samun nasarar cika alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

Sarakunan su ne na Kano, Rano, Karaye, Gaya, da Bichi wanda ake zargin an kawo domin su kishiyanci Malam Muhammadu Sanusi II.

A karshe gwamnatin APC ta cirewa Muhammadu Sanusi II, ta nada Aminu Ado Bayero, yanzu wasu suna kawo shawarar dawo da shi.

Kara karanta wannan

Abba ya nunawa duniya masoyansa a Kano da ya dawo bayan hukuncin Kotun Koli

Za a dawo da Sanusi II gidan sarauta?

An ji labari cewa mahaifiyar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ta ziyarci mahaifiyar Khalipha Muhammadu Sanusi bayan hukuncin kotu.

Uwar gwamnar ta yi addu’ar Allah ya dawo da Muhammadu Sanusi II gidan Dabo domin cigaba da ayyukan alherin da ya fara a mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel