Ganduje Da Dalilai 5 Da Suka Yaudari APC, A Karshe Abba Ya Tsare Kujerarsa a Kotun Koli

Ganduje Da Dalilai 5 Da Suka Yaudari APC, A Karshe Abba Ya Tsare Kujerarsa a Kotun Koli

  • Zaman Abdullahi Umar Ganduje shugaban APC ya sa wa ‘yan APC rai cewa za su koma gidan gwamnati a Kano
  • Duk da nasarar NNPP a zabe da galabar ‘yan majalisarta a kotu, Nasiru Gawuna ya san rai zai yi mulki a bana
  • Magoya bayan APC har sun fara farin ciki sai murnar ta koma ciki da alkalan kotun koli su ka soke tsige NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Jam’iyyar APC tayi tunanin ita za ta samu nasara a kotun koli a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano na 2023.

A karshe an ji labarin abin da ya faru, duk alkalan da su ka saurari karar su ka tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida ya aika muhimmin sako ga Gawuna bayan hukuncin Kotun Koli

Daily Trust ta jero abubuwan da su ka taimakawa APC wajen samun kwarin gwiwa a shari’arta da Abba Gida Gida.

NNPP.
NNPP da APC a Kano Hoto: @KwankwasoRM, @Dawisu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Abdullahi Umar Ganduje

Tun kafin ya bar mulki, Abdullahi Umar Ganduje ya sa wa APC rai cewa ba za ta rasa Kano ba, da aka tafi kotu, ya nuna mata za a karbi mulki.

Bayan zamansa shugaban jam’iyya, APC ta yi nasara a kotun korafin zabe da daukaka kara, Abdullahi Ganduje ya fito ya nuna kusantowar nasara.

2. Hadimai da manyan APC

Jagorori da hadiman APC da yawa sun rika nunawa magoya baya za a karbe mulki daga hannun gwamnatin APC, Nasiru Gawuna ya karbe iko.

3. Raba ankon Gawuna

Bayan hutun sabuwar shekara, sai lamarin ya kai wani mataki har ta kai ana rabon kaya da hulunan anko da sunan bikin rantsar da Nasiru Gawuna.

Kara karanta wannan

Nasarar Kotun koli: Abin da Kwankwaso ya fada a kan Abba da yarjejeniya da APC

4. Gyaran hedikwatar APC a Kano

Jaridar ta ce da APC ta fara gyara hedikwatarta na reshen jihar Kano, sai aka yi tunanin alamar komawa gidan gwamnati ne bayan hukuncin kotun koli.

5. APC ta shirya motoci da jirage

Majiyarmu ta ce ‘yan APC sun shirya motoci da za ayi amfani da su wajen dauko Nasiru Gawuna da ‘yan tawagarsa idan sun shigo Kano bayan hukunci.

Ana daren da za ayi hukunci, mun fahimci jagororin APC sun yanki tikitin jiragen sama daga Abuja zuwa Kano, kwatsam labari ya canza a kotun koli.

Kwankwaso ya yi magana bayan nasarar NNPP

A karon farko, ana da labari Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan zargin yin wani sulhu kafin Abba Kabir Yusuf ya iya samun nasara a kotu.

Kotun koli ta tabbatar da NNPP a kan mulki, jagoran Kwankwasiyya ya ce kowa ya dauki darasi, a nan yi batun alakarsa da Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Yadda Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abba a kan Gawuna da APC a zaben Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel