Alamu Sun Nuna Abba Ya Karaya a Shari’ar Zaben Gwamna - Tsohon Hadimin Ganduje

Alamu Sun Nuna Abba Ya Karaya a Shari’ar Zaben Gwamna - Tsohon Hadimin Ganduje

  • Salihu Tanko Yakasai ya soki yadda Abba Kabir Yusuf ya tunkari shari’ar zaben gwamnan Kano na 2023
  • Tsohon hadimin na Abdullahi Umar Ganduje ya zargi gwamna mai-ci da yin sakaci da shari’ar zabensa
  • Da yake magana a dandalin Twitter, Dawisu ya nuna rauni ne jagororin gwamnati su buge da zanga-zanga

Abuja - Ana shari’a gaban alkalai a kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya tofa albarkacin bakinsa.

Alhaji Salihu Tanko Yakasai wanda ya yi takarar gwamna a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar SDP, ya bayyana kuskuren da NNPP ta yi.

Ganin yadda shari’ar zaben 2023 ta ke gudana tsakanin APC da NNPP, ‘dan takaran da ya sha kashi ya na ganin abubuwa za su iya rikida.

Gwamna Abba Kabir Yusuf a Kano
Gwamna Abba Gida Gida da sauran manyan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sakacin Gwamna Abba Kabir Yusuf

Kara karanta wannan

Yadda Ganduje Ya Dawo Cikin Lissafin Siyasa, Ya Wargaza Kawancen Kwankwaso-Tinubu

Yayin da ake sauraron karar, Salihu Yakasai ya ce lauyoyin gwamna Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar NNPP ba su maida hankali da kyau ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ‘dan siyasar, shaida guda kurum gwamna mai-ci ya aika domin ya kare shi a gaban kotu har aka kammala sauraron kowane bangare.

Zanga-zanga da salloli na musamman

Makonni da gama sauraron kara, ana jiran a soma yanke hukunci, sai aka ji gwamnatin Kano za ta shirya zanga-zanga a kan shari’ar.

A karshen makon jiya, aka jagoranci wata sallah ta musamman domin neman zaman lafiya da nasara a shari’ar zaben gwamna da ake yi.

Salihu Yakasai wanda ya yi aiki da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya ce duk wadannan sun nuna gwamna Abba Yusuf ya soma karaya.

Sai dai wasu sun maida masa martani a shafin Twitter inda ya yi maganar, su ka ce aikin wanda ya shigar da kara ne ya yi ta gabatar da hujjoji.

Kara karanta wannan

Makiya Kano Za Su yi Amfani da Kotu, A Tsige NNPP a Dawo da APC - Malamin Addinin Musulunci

“Ina mamakin yadda Gwamna Abba yaki tsayawa ya kare kujerar sa a kotu, ya ki tura shaidu sai mutum daya, ya ki yin iya abin da zai yi a lokacin da ake shari'a.
Sai yanzu yake shirya zanga zanga, da taron addu'a. Kana da gwamnati kana irin wadannan abubuwan, wannan alamar karaya ce.”

- Salihu Tanko Yakasai

"Ana kan kokarin maido APC kan mulki"

Rahoto ya zo cewa Dr. Sani Ashir ya zargi wasu da ya ce makiyan jihar Kano ne da kokarin karbe nasarar jam'iyyar NNPP a kotun karar zaben 2023.

Idan NNPP ta yi rashin sa’a, za a iya yin waje da Gwamna Abba Kabir Yusuf da bayan watanni uku a kan mulki, hakan zai iya ba kowa mamaki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng