Kano: Abba Gida-Gida Ya Aika Muhimmin Sako Ga Gawuna Bayan Hukuncin Kotun Koli

Kano: Abba Gida-Gida Ya Aika Muhimmin Sako Ga Gawuna Bayan Hukuncin Kotun Koli

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira da a samar da hadin kai a jihar Kano yayin da ya roki abokan adawa da su zo su yi aiki tare
  • Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da Kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige shi daga kujerarsa
  • Gwamna Yusuf ya mika godiyar sa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan rashin tsoma bakinsa a harkokin shari'a

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Bayan ya yi nasara a Kotun Koli. Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya yi kira ga babban abokin hamayyarsa na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da su zo su yi aiki tare.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan Abba ya faɗi gaskiya kan tsoma bakin Shugaba Tinubu a hukuncin kotun ƙoli

A ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, Yusuf, wanda ya lashe zabe karkashin inuwar jam’iyyar NNPP ya gayyaci Gawuna da jam’iyyar APC mai adawa a jihar, da su zo su hada hannu wajen kawo ci gaba a jihar.

Abba ya aika sako ga Gawuna
“Ka Zo Mu Gina Kano Tare”: Abba Ya Aika Muhimmin Sako Ga Gawuna Hoto: Abba Kabir Yusuf/Nasir Gawuna
Asali: Facebook

Cikin yanayi na farin ciki, gwamnan ya nuna shirinsa na yin sulhu da babban abokin hamayyar nasa yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya shafe kimanin watanni bakwai yana fafatawa a kotu domin kare kuri’unsa, inda ya sha kaye a kotun zabe da kotun daukaka kara, kwatsam sai Kotun Koli ta dawo masa da kujerarsa.

Gwamnan ya nuna godiyarsa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima kan rashin nuna son kai.

Ya bayyana cike da gamsuwa cewa Shugaban kasar ya ki tsoma baki a hukuncin Kotun Koli, duk da matsin lamba da ya dunga fuskanta daga bangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

Nasarar Kotun koli: Abin da Kwankwaso ya fada a kan Abba da yarjejeniya da APC

Ya ce:

“A matsayina na dan dimokradiyya kuma mai son ci gaba, ina kira ga abokin hamayya na da magoya bayansa da su hada hannu da ni wajen fafutukar ganin an bunkasa jiharmu ta Kano, domin ci gaban al’ummarta.
“Kanawa na bukatar shugabanni masu hangen nesa, kishi da jajircewa wajen aiwatar da ayyuka, manufofi da tsare-tsare wadanda ke da tasiri kai tsaye a rayuwarsu ta kowane bangare kuma a fadin lungu da sako na jihar.”

Abba ya jinjinawa Kwankwaso

Gwamnan ya yi godiya ga Allah kan nasarar da ya samu sannan ya yaba ma Kanawa kan goyon bayansu, jajircewa, addu’o’i da sadaukarwarsu, rahoton The Cable.

Ya yabawa bangaren shari’a tare da godiya ga alkalan kotun koli kan daukaka darajar shari’a ta hanyar tabbatar da zaben sa.

Gwamna Yusuf ya kuma yi godiya ga shugabannin NNPP a dukkan mayakai, inda ya mika godiya ta musamman ga tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan gudunmawa da jagorarsa a lokacin da yake cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci, ya gode wa wanda ya ba shi nasara

Kwankwaso ya magantu kan hukuncin Kotu a Kano

A gefe guda, mun ji cewa Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, ya bayyana cewa shari'ar zaben gwamnan jihar Kano darasi ne ga kowa.

Kwankwaso, wanda ya kasance ubangidan Gwamna Abba Kabir Yusuf a siyasa, ya ce hukuncin Kotun Kolin ya dawo da muradin mutanen jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel