APC Ta Bayyana Babban Dalilin da Ya Sa Ta Ke Samun Nasara a Zabuka, Ta Yi Alkawari Ga 'Yan Kasa

APC Ta Bayyana Babban Dalilin da Ya Sa Ta Ke Samun Nasara a Zabuka, Ta Yi Alkawari Ga 'Yan Kasa

  • Jam'iyyar APC ta bayyana irin shirin da take yi a ko wane zaben don tabbatar da nasarar ta ba tantama
  • Kungiyar gwamnonin APC ta ce kullum jami'yyar a shirye ta ke don tunkarar ko wane zabe a ko wane lokaci
  • Gwamnonin sun bayyana haka yayin ganawa da manema labarai bayan taronsu a Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Gwamnonin Najeriya a jam'iyyar APC sun yi alfahari kan zaben da za a gudanar, Arise TV ta tattaro.

Gwamnonin karkashin kungiyar PGF sun ce kullum jami'yyarsu a shirye ta ke don tunkarar ko wane irin zabe a kasar a ko wane lokaci.

Kara karanta wannan

Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5

APC ta bayyana babbar dalilin nasararta a zabuka
APC ta ce a shirye ta ke don tunkarar ko wane zabe. Hoto: @Angelgabbyshara.
Asali: Twitter

Mene APC ke cewa kan zabuka?

Gwamnonin sun bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja ta bakin shugabansu, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uzodinma ya ce jami'yyarsu a kullum jira take ko wane zabe ya zo saboda kullum a shirye suke kafin ma zuwan zaben, cewar Leadership.

Sai dai Uzodinma bai bayyana karara ko taron da suka gudanar ya shafi shirye-shiryen zaben da za a gudanar a wannan shekara ba.

Idan ba a mantaba, Hukumar INEC ta sanya 3 ga watan Faburairun wannan shekara a matsayin ranar gudanar zaben cike gurbin wasu kujeru.

Har ila yau, a ranar 21 ga watan Satumba za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo sai na jihar Ondo a watan Oktoba.

Wane alkawari APC ta yi?

Uzodinma ya ce wannan shi ne taronsu na farko a wannan shekara inda ya ce sun hadu ne don hada gwiwa da Gwamnatin Tarayya kan dakile matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama Khadija Manzo da wasu 15 kan fataucin yara, sun ceto jarirai 3 a jihar arewa

Har ila yau, sun tattauna yadda za a hada kai don kawo cigaba mai dorewa a kasar baki daya.

Ya ce:

"Jamiyyarmu kullum a shirye ta ke don fafatawa a ko wane zabe, mun hada kai don mara wa gwamnatin APC baya.
"Za mu ci gaba da mara wa shugaban kasa, Bola Tinubu baya don kawo ci gaba a kasar baki daya."

Ganduke ya taya gwamnan APC murna

A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue kan nasara a Kotun Koli.

Ganduje ya roki jami'yyun 'yan adawa da su mara wa gwamnan baya don inganta rayuwar al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel