Kotun Koli Ta Raba Gardama a Shari'ar Zaben Gwamnan APC a Jihar Arewa

Kotun Koli Ta Raba Gardama a Shari'ar Zaben Gwamnan APC a Jihar Arewa

  • Kotun ƙoli ta zartar da hukuncin ƙarshe kan taƙaddamar zaɓen gwamnan jihar Benue tsakanin Gwamna Hyacinth Alia da Titus Uba na jam'iyyar PDP
  • Kotun ƙolin a hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, ta tabbatar da nasarar da Gwamna Alia na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar
  • Kotun mai alƙalai biyar ta kuma yi watsi da ƙarar da Titus Uba da jam'iyyarsa ta PDP suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Gwamna Alia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ƙoli da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC.

A ranar Litinin, 8 ga watan Janairu kotun ƙoli ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta a zaɓen gwamnan Benue, Titus Uba, suka yi, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Kotun koli: Ana dab da yanke hukunci dan takarar gwamnan APC ya mika sabuwar bukata

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Alia
Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue Hoto: Emmanuel Ter
Asali: Twitter

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna da kotun ɗaukaka ƙara a Abuja sun tabbatar da zaɓen Hyacinth Alia na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin gamsuwa da hukuncin ya sanya Titus Uba da PDP suka garzaya zuwa kotun ƙoli.

Yadda zaman kotun ya kaya

Kotun mai alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ta yi hukunci cewa batutuwan da aka gabatar a ɗaukaka ƙarar ba su cancanci zama abubuwan bayan zaɓe ba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Kotun ta buƙaci lauyan jam'iyyar PDP da Titus Uba, Sebastine Hon (SAN) da ya janye ƙarar da aka ɗaukaka ta farko, inda ya yi hakan, sannan daga bisani kotun ta yi watsi da ita.

Mai shari’a Okoro ya ce, kamar yadda ɓangarorin suka amince, umarnin korar da aka yi dangane da ɗaukaka ƙarar farko mai lamba: SC/CV/1162/2023 zai shafi ta biyu, mai lamba: SC/CV/1164/2023.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni, sanatoci da yan majalisar da za su dawo APC

Kotun Ƙoli Ta Tanadi Hukunci

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ƙoli ta tanadi hukunci a shari'ar neman tsige Gwamna Nwifuru na jihar Ebonyi.

Kotun ƙolin ta tanadi hukuncin ne bayan ta saurari bayanai daga bakin lauyoyin ɓangarorin biyu, inda ta sanar da su cewa za ta tuntuɓe su kan ranar da za ta yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel