Sabuwar Rigima Ta Barke Tsakanin Jam'iyyar APC Da Gwamnanta Kan Abu 1

Sabuwar Rigima Ta Barke Tsakanin Jam'iyyar APC Da Gwamnanta Kan Abu 1

  • Gwamna Hyacinth Alia ya dakatar da zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Benue
  • Zaɓen fidda gwanin na ɗan takarar jam’iyyar APC ne a zaɓen cike gurbi da za a yi ranar 4 ga watan Fabrairu a kujerar da ba kowa a mazaɓar Guma 1 ta jihar
  • Alia ya ce zaɓen fidda gwanin na jam’iyyar APC ba za a iya gudanar da shi ba saboda barazana da ƙwacen da wasu masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Guma, jihar Benue - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta caccaki gwamna Hyacinth Alia kan dakatar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar na zaɓen cike gurbi da za a yi ranar 4 ga watan Fabrairu a jihar Benue.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni, sanatoci da yan majalisar da za su dawo APC

Zaɓen shi ne na cike gurbin kujerar ɗan majalisar dokoki ta jihar na mazaɓar Guma 1 bayan naɗin Dakta Yamar Ortese a matsayin kwamishinan lafiya da ayyukan jin kai, inji rahoton Daily Trust.

Rigima ta kunno kai tsakanin Gwamna Alia da APC
Gwamna Alia ya dakatar da zaben fidda gwani na jam'iyyar APC Hoto: Emmanuel Ter
Asali: Facebook

Gwamnan a wani taron manema Labarai a ranar Asabar, ya dakatar da zaɓen fidda gwanin na jam’iyyar APC inda ya bayyana barazanar da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi, waɗanda ba ƴan ƙaramar hukumar Guma ba ne, kuma ba za su shiga zaɓen ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Alia ya dakatar da zaɓen?

A kalamansa:

"Tsaron jihar nan yana da matuƙar amfani a gare mu. Jam’iyyar APC za ta gudanar da zaɓen fidda gwani amma ta fuskanci rashin da’a wanda hakan ya jawo barazanar rashin tsaro a Guma. Ya zama wajibi mu kwantar da hankulan fusatattun matasan.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya tsoma baki, ya fallasa shirin APC na ƙwace mulki daga gwamna mai ci

"Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun ji takaici. Ba zan so wani kamannin rashin tsaro a jihar ba. Na dakatar da zaɓen fidda gwani na deliget.
"Abin baƙin ciki ƴan jam'iyya sun fito amma mutanen da ba ƴan jam'iyyar ba sun dakatar da su a ƙofar shiga. Dukkanin masu ruwa da tsaki an dakatar da su sannan matasa sun fusata. Ya kamata dole ƴan jam'iyya su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a jiha."

Wane martani jam'iyyar APC ta yi?

Sai dai kakakin jam'iyyar APC a jihar, Morgan Ihomun, ya ce Gwamna Alia ba zai iya dakatar da zaɓen da jam'iyyar ta riga ta gudanar "bisa tsari."

Morgan yace an gudanar da zaɓen fidda gwani kuma ɗan takara ya fito.

"Tambayar da ya kamata mu yi ita ce, shin gwamna yana da ikon dakatar da zaɓen fidda gwani?"

Gwamna Alia Ya Magantu Kan Shirin Barin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi magana kan shirin komawarsa jam'iyyar PDP.

Gwamnan ya musanta wannna jita-jitar inda ya ƙara tabbatar da cewa a shirye yake domin cigaba da sanya jam'iyyar APC alfahari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel