Yan Sanda Sun Kama Khadija Manzo da Wasu 15 Kan Fataucin Yara, Sun Ceto Jarirai 3 a Jihar Arewa

Yan Sanda Sun Kama Khadija Manzo da Wasu 15 Kan Fataucin Yara, Sun Ceto Jarirai 3 a Jihar Arewa

  • Jami'an rundunar yan sanda a jihar Gombe sun bankado wata ma'aikata ta fataucin jarirai a yankin Barunde
  • Rundunar tsaron ta ce ta kama wata mai suna Khadija Manzo tare da wasu mutum 15 da ake zargi da hannu a wannan aika-aikar
  • An kuma yi zargin cewa ana aikatawa mata fyade domin su samu ciki su haihu sannan a siyar da yaran ga masu bukata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Rundunar yan sandan jihar Gombe ta ce ta kama wasu mutane 16 kan zargin fataucin kananan yara a jihar, jaridar The Cable ta rahoto.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, Mahid Abubakar, kakakin yan sandan jihar, ya ce al'ummar Barunde ne suka kai wa rundunar kara.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da yan bindiga suka yi garkuwa da mutum 85 a hanyar Kaduna-Abuja

Yan sanda sun kama masu fataucin jarirai a Gombe
Yan Sanda Sun Kama Khadija Manzo da Wasu 15 Kan Fataucin Yara, Sun Ceto Jarirai 3 a Jihar Arewa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ya ce jami'an da suka farmaki wajen sun gano cewa wadanda ake zargin suna gudanar da wata masana'anta ta siyar da jarirai ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar ana ajiye mata a masana'antar domin su haihu sannan a siyawar mutane da jariran da aka haifa a bangarori daban-daban na kasar.

Abubakar ya bayyana cewa jami'an tsaron sun yi nasarar ceto wasu jarirai uku, yayin da tuni aka yi fataucin wasu biyu zuwa Lagas da Anambra, rahoton Sahara Reporters.

Me yan sanda suka bankado game da lamarin?

A yayin gudanar da bincike, yan sandar sun gano cewa an siyar da daya daga cikin jariran ga wani mazaunin Gombe ta hannun wata ma'aikaciyar jin kai, kan kudi N400.000.

Har ila yau, Abubakar ya ce rundunar ta kuma samu rahoton cewa wata uwa ta siyar da jaririnta ga masu fataucin yaran, yana mai cewa akwai kuma batun yi wa mutane fyade a masana'antar.

Kara karanta wannan

Abinda ya sa aka yi musayar wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja, Yan Sanda sun magantu

Kakakin yan sandan ya ce:

"Wannan wani laifi ne na hada baki da fataucin yara inda aka kama wata Khadija Manzo da wasu 15 sakamakon wani bayanan sirri da aka samu daga al'ummar Barundde a karshen mako.
“Cewa a wani lokaci a shekarar da ta gabata, wata Khadija Manzo da wasu 15 sun shiga harkar sayar da jarirai ga mabukata.
"Da samun rahoton, jami'an tsaron sashin Lowcost sun gudanar da bincike wanda ya kai ga kama Manzo da sauran wadanda ake zargin."

Mai magana da yawun yan sandan ya kuma ce a yayin bincike, an gano cewa Manzo ta sayar da jarirai biyu ga Ukamaka Ugwu a lokuta daban-daban.

Za su gurfana a kotu

Ya ce an kama sauran wadanda ake zargi da hannu a wannan aika-aika, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kotu.

Sarkin Kano ya magantu kan fataucin yara

Kara karanta wannan

Bayan kama 8, Asirin masu hannu a kisan bayin Allah sama da 150 ya ƙara tonuwa a arewa

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo a baya cewa mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi tir da yawan sace-sacen yara kanana daga yankin Arewa zuwa Kudu.

Basaraken ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake yawan sace-sacen mutane a yankin arewacin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel