Wasu ‘Yan Jam’iyyar PDP da ke Goyon Bayan Gwamnatin Tinubu a Boye ko a Zahiri

Wasu ‘Yan Jam’iyyar PDP da ke Goyon Bayan Gwamnatin Tinubu a Boye ko a Zahiri

  • Ana zargin kafafun wasu ‘yan jam’iyyar PDP ya tsallaka zuwa APC, akwai yiwuwar su canza sheka
  • Reno Omokri yana cikin wadanda ake gani za su iya barin PDP saboda yadda su ke ta kare Bola Tinubu
  • Nyesom Wike ya yi wa Tinubu aiki a zaben shugaban kasa, har minista aka ba shi duk da yana 'dan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Akwai wasu ‘yan adawa musamman na jam’iyyar PDP mai hamayya da su ke yawan fitowa su na kare Bola Ahmed Tinubu.

Rahoton nan ya kawo jerin kusoshin jam’iyyar PDP da su ke ba gwamnatin APC kariya:

PDP - @renoomokri, @BwalaDaniel
Mutanen PDP da yabon APC Hoto: @renoomokri, @BwalaDaniel
Asali: Twitter

1. Nyesom Wike

Nyesom Wike yana cikin wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a kan PDP a zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Hadiman Atiku 5 da su ka juya masa baya, suka yi aiki da Gwamnati da APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan APC ta doke Atiku Abubakar da Peter, sabon shugaban Najeriyan ya zabi Nyesom Wike ya zama ministan harkokin birnin tarayya.

Tsohon gwamnan na Ribas yana fada cewa har gobe bai da-na-sanin goyon bayan Tinubu a maimakon Atiku Abubakar na jam’iyyarsa PDP.

2. Reno Omokri

Reno Omokri ya fito karara ya marawa Atiku Abubakar baya da ya fito takarar shugaban kasa a 2023, musamman a shafukan zamani.

Faston yana yawan yaban Bola Tinubu, an ji ya ce a mako guda, shugaban kasa ya yi abin da ya gagari Muhammadu Buhari a shekaru takwas.

Omokri wanda ya taba zama hadimin Goodluck Jonathan ya saba cacaccakar magoya bayan Peter Obi wajen kare gwamantin Tinubu.

3. Daniel Bwala

Ba a dade da jin Daniel Bwala ya na caccakar gwamnatin APC ba, a cewarsa duk shekarun da Tinubu zai yi a ofis, ba za a ga cigaba ba.

Kara karanta wannan

"Sai dai ayi abin da za ayi", Mutumin Atiku ya ce ya koma goyon bayan Tinubu

Ba a dade da wannan magana ba sai aka ji jigon na PDP mai adawa ya zauna da Bola Tinubu, har yana cewa zai goyi bayan gwamnatinsa.

Tsohon mai magana da yawun na Atiku ya fito a X ya yabi shugaban kasa bayan dakatar da Betta Edu da rage kashe kudin tafiye-tafiye.

APC v Abba Gida Gida a Kano

Yayin da za ayi hukunci a kotun koli, an ji APC ta na sa ran a tsige Abba Kabir Yusuf wanda hukumar INEC ta ba nasara a zaben 2023.

A baya an ji wasu cikin jagororin jam’iyyar APC na reshen Kano irinsu Abba Dala da Auwalu Lawan Aranposu su na sukar Nasiru Gawuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel