Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Ya Fadi Abu 11 da Tinubu Ya Yi a Mako Daya Wanda Buhari Ba Zai Iya Ba

Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Ya Fadi Abu 11 da Tinubu Ya Yi a Mako Daya Wanda Buhari Ba Zai Iya Ba

  • Reno Omokri, hadimin tsohonb shugaban kasa kuma jigon PDP, ya lissafa wasu abubuwa 11 da Shugaban kasa Tinubu ya cimmawa a cikin mako guda
  • Jigon na PDP ya jadadda cewar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya cimma wadannan abubuwa cikin kankanin lokaci ba
  • Sai dai kuma, Omokri ya ce Tinubu ba ya zayyana nasarorin da ya samu, inda ya ce hakan ba zai shafi shugaban kasar kadai ba, har ma da martabar kasar gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya yaba ma Shugaban kasa Bola Tinubu kan manyan matakan da ya dauka kan al’amuran kasar cikin mako guda.

Omokri ya yaba ma Tinubu kan dakatar da ministar jin kai da yakar talauci, Betta Edu kan badakalar kudi naira miliyan 585 a ma’aikatarta.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Shekarau ya yaba, ya fadi abin da ya ragewa Tinubu ya aikata a ofis

Reno Omokri ya yi shagube ga Buhari yayin da ya yabi Tinubu
Betta: Tinubu ya yi abun da zai dauki Buhari shekara a cikin mako 1 – Hadimin tsohon shugaban kasa Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Reno Omokri, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa, wadannan nasarori guda 11 da Tinubu ya samu cikin mako guda da ace magabacinsa ne, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, da sai ya shafe tsawon shekara guda kafin ya cimma masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omokri ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, yayin da yake tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a sansanin shugaban kasar cikin yan kwanaki da suka gabata.

Nasarorin da Tinubu ya samu a mako guda

Ga jerin abubuwa 11 da Tinubu ya cimma cikin mako guda, kamar yadda Omokri ya bayyana:

  1. Ya dakatar da ministar da ta yi kuskure
  2. Ya sammaci wani minista kan wata kwangila mai cike da takaddama
  3. Ya rage tafiye-tafiyensa tare da rage yawan kashe kudi
  4. Ya kori wasu shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu saboda sakaci
  5. Ya dauki mataki kan kwalin digiri da ake samu cikin mako guda ta hanyar saka takunkumi a Benin da sauran kasashe
  6. Ya bayyana shirin gina sabuwar masana'antar karafa a Najeriya
  7. Ya kaddamar da shafin yin fasfot kai tsaye ta yanar gizo
  8. Ya biya bashin zunzurutun kudi har biliyan 12 ga Super Eagles da sauran tawagar kasa
  9. Ya fara biyan tallafin albashi ga ma'aikatan gwamnati
  10. biya Naira biliyan 105.5 don gyaran tituna 266
  11. shiga tsakani don samar da zaman lafiya a Saliyo bayan yunkurin juyin mulkin da aka dakile

Kara karanta wannan

Ba kamar Buhari ba, Tinubu ya dauki mataki kan yawan kashe kudade a tafiye-tafiye, ya fadi dalili

Kotu ta garkame tsohon minista

A wani labarin, mun ji cewa hukumar EFCC, ta gurfanar da Olu Agunloye, tsohon ministan wutar lantarki da karafa, a gaban kuliya bisa zarginsa da aikata zamba.

EFCC na binciken Agunloye kan kwangilar wutar lantarkin Mambilla da kudinta ya haura dala biliyan 6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel