Hadiman Atiku 5 da Su Ka Juya Masa Baya, Suka Yi Aiki da Gwamnati da APC

Hadiman Atiku 5 da Su Ka Juya Masa Baya, Suka Yi Aiki da Gwamnati da APC

  • Ana ganin hadimai da mukarraban Atiku Abubakar sun ci amanarsa, sun rika bin gwamnati mai-ci
  • Irinsu Malam Garba Sheu sun rabu da tsohon mataimakin shugaban kasar kuma jagoran adawar
  • Michael Achimugu ya rika fadin munanan kalamai a game da Wazirin Adamawa da aka raba jiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wasu na kusa da Atiku Abubakar a lokacin yana mulki har zuwa yanzu sun rika barin shi a lokacin da yake bukatarsa.

Rahoton nan ya dauko jerin wasu da ake ganin na kusa da Atiku Abubakar ne da su ka bi Muhammadu Buhari ko Bola Tinubu.

Atiku
Mutanen Atiku sun bi APC Hoto: @BwalaDaniel, @Atiku, @GarShehu
Asali: Twitter

1. Daniel Bwala

A ranar Laraba, 10 ga watan Junairu, 2024, Daniel Bwala ya yi zama da Bola Tinubu, kuma ya tabbatarwa Duniya zai mara masa baya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP zai bada gudumuwa wajen goyin bayan gwamnatin APC bayan yana cikin masu magana da yawun Atiku Abubakar a 2023.

2. Michael Achimugu

Ana da labarin Michael Achimugu wanda Atiku Abubakar ya saki jiki da shi tamkar yaro da ubansa, sai daga baya labarin alakarsu ya canza.

Lokacin kamfe a 2023, Achimugu ya ce za a ga rashin gaskiya idan aka yi kuskuren zaben uban gidansa, daga baya ya zama Darekta a NCAA.

3. Garba Shehu

Garba Shehu ya yi aiki da Atiku Abubakar a lokacin yana mataimakin shugaban kasa a mulkin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.

Da Muhammadu Buhari ya karbi shugabancin Najeriya a 2015, sai ya dauko Malam Garba Shehu, ya nada a matsayin mai magana da yawunsa.

4. Prince Kassim Afegbua

Prince Kassim Afegbua ya taba zama kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben 2019, shi ma daga baya ya yi fatali da shi.

Kara karanta wannan

"Sai dai ayi abin da za ayi", Mutumin Atiku ya ce ya koma goyon bayan Tinubu

Tsohon kwamishinan ya taimaka wajen yakar Wazirin Adamawa a 2023, bai rike da mukami a yanzu, amma yana takarar gwamna a APC.

Mutanen Atiku da ba su PDP a yau

Legit ta kawo labarin irinsu Dr. Umar Ardo wanda ya yi aiki da Atiku Abubakar amma daga baya ya koma goyon bayan Muhammadu Buhari.

Dr. Usman Bugaje yana cikin masu ba Atiku shawara da yake mulki, daga baya sun raba jiha da 'dan siyasar ya zauna a APC kafin ya koma PRP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel