"Sai Dai Ayi Abin da Za Ayi", Mutumin Atiku Ya Ce Ya Koma Goyon Bayan Tinubu

"Sai Dai Ayi Abin da Za Ayi", Mutumin Atiku Ya Ce Ya Koma Goyon Bayan Tinubu

  • Daniel Bwala ya kama hanyar barin PDP, zai koma jam’iyyar APC mai mulki da ya bari a 2022
  • ‘Dan siyasar da ya yaki takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa ya yi watsi da Atiku Abubakar
  • Bwala ya fadawa duniya ya shirya sauya-sheka saboda goyon bayan Mai girma Bola Tinubu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jagora a jam’iyyar hamayya ta PDP, Daniel Bwala, ya tabbatar da cewa zai marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Bayan zaman Daniel Bwala da mai girma shugaban kasa, Punch ta ce ya fito a mutum ya nuna zai iya canza sheka zuwa APC.

Bwala - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Daniel Bwala ya bi Bola Tinubu Hoto: Bwala Daniel, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daniel Bwala zai bar Atiku da PDP?

Lauyan ya ce zai goyi bayan gwamnatin Bola Tinubu ko da hakan yana nufin zai fice daga babbar jam’iyyar hamayya watau PDP.

Kara karanta wannan

Hadiman Atiku 5 da su ka juya masa baya, suka yi aiki da Gwamnati da APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yammacin Laraba ne ‘dan siyasar ya hadu da Mai girma Bola Tinubu a Aso Rock Villa, dama an fara rade-radin zai canza gida.

Ziyarar da Bwala ya kai wa Tinubu ta jawo surutu a kafafen sanarwa inda aka ji ana labari ana zarginsa da cin amanar Atiku Abubakar.

The Cable ta rahoto abin da Bwala ya shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasar.

Jawabin Daniel Bwala a Aso Villa

"Na fada masa yau, a shirye nake in bada gudumuwa ta wajen goyin bayan gwamnatin nan, kuma ban bukatar ba kowa hakuri.
APC jam’iyyar siyasa ce. Bola Tinubu ne yake ba ni kwarin gwiwa; idan mara masa baya za ta maida ni APC, to shikenan”

- Daniel Bwala

Bwala ya bar APC zuwa jam’iyyar PDP ne da sunan an tsaida musulmi da musulmi, don haka ya bi bayan takarar Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

‘Dan takaran shugaban kasar ya nada Bwala a matsayin mai magana da yawunsa.

Legit ta rahoto yadda aka ji Bwala ya fara kokarin yabon gwamnatin APC a makon nan.

Kafin nan tsohon mai ba APC shawara a kan harkar shari’ar ya nuna Wazirin Adamawa zai sake takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Bwala ya ce Tinubu zai yi 8

A baya an rahoto Daniel Bwala yana cewa Shugaba Bola Tinubu zai iya yin shekara 8 a kan mulki idan ba a dauki mataki tun yanzu ba.

Jigon PDP ya yi hasashen abin da zai iya faruwa idan jam'iyyun adawa suka ki hada kai a 2027, ya ce ta haka ne za a iya karbe mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel