Babban Ministan Shugaba Tinubu Zai Yi Murabus, Bayanai Sun Fito

Babban Ministan Shugaba Tinubu Zai Yi Murabus, Bayanai Sun Fito

  • A watan Nuwamba ne kotun ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin kotun da ta bayyana Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Plateau ta Kudu
  • Daga bisani, tsohon gwamnan ya karɓi takardar shaidar cin zaɓe daga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC)
  • Yanzu haka wata jarida ta ruwaito cewa Lalong zai bar majalisar ministocin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koma majalisar dattawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Idan dai ba wani sauyi aka samu ba, Simon Lalong, ministan ƙwadago da samar ayyuka, zai yi murabus daga muƙaminsa na yanzu.

A ranar 7 ga watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja, ta tabbatar da hukuncin kotun da ta bayyana ministan ya lashe zaɓen sanatan Plateau ta Kudu da aka gudanar a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kitsa rikicin Wike da Gwamna Fubara? Gaskiya ta bayyana

Lalong zai yi murabus daga mukamin minista
Simon Lalong ya fi son mukamin Sanata Hoto: Rt. Hon. Simon Bako Lalong
Asali: Facebook

Simon Lalong ya fi son Majalisar Dattawa

A ranar 23 ga watan Nuwamba, Lalong ya karɓi takardar shaidar cin zaɓe a matsayin zaɓaɓɓen sanata a majalisar dattawa ta 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, majiyoyi na kusa da ministan, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Plateau sun bayyana cewa nan ba da jimawa ba (Lalong) zai yi murabus daga mukaminsa ya zama Sanata.

Jaridar Leadership ta ambato wani majiya na cewa:

"Ba da jimawa ba Ministan zai koma Majalisar Dattawa. Zai je can ne domin tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya samu nasara. Majalisar dattawa ita ce dattawa suke kuma yana son shiga cikinsu."
"Mai girma shugaban ƙasa zai naɗa sabon matashi a matsayin minista mai wakiltar jihar Plateau domin maye gurbin mai girma Hon. Simon Bako Lalong, mai girma ministan kwadago da samar da ayyuka da zarar ya yi murabus."

Kara karanta wannan

Farfesa Yakubu ya rantsar da sabbin shugabannin INEC na jihohi 9, ya tsallake guda ɗaya

"Kun san irin rawar da ministan ya taka a lokacin yaƙin neman zaɓe, ya yi imani da Asiwaju kuma a shirye yake ya ba da gudunmawa domin ganin gwamnatinsa ta samu nasara."

Lalong Ya Shiga Ruɗani Kan Muƙamin Sanata da Minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan ƙwadago da samar da ayyuka, Simon Bako Lalong, ya shiga ruɗani kan muƙamin da zai zaɓa a tsakanin minista ko sanata.

Lalong wanda kotu ta tabbatar a matsayin zaɓaɓɓen sanatan Plateau ta Kudu yana tantama kan ko ya cigaba da zama a muƙamin minista ko ya koma majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel