Kotu Ta Ayyana Simon Lalong Matsayin Wanda Ya Lashe Kujerar Sanatan Filato Ta Kudu

Kotu Ta Ayyana Simon Lalong Matsayin Wanda Ya Lashe Kujerar Sanatan Filato Ta Kudu

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a Jos babban birnin jihar Filato ta karɓe kujerar sanatan PDP
  • Kotun ta hannanta kujerar ga tsohon Gwamnan jihar Simon Lalong na jam'iyyar APC
  • Lalong na dai ɗaya daga cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin ministocinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jos, jihar Filato - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a birnin Jos na jihar Filato, ta ƙwace kujerar sanatan jam'iyyar PDP Napoleon Bali da ke wakiltar Filato ta Kudu.

Bayan kwace kujerar, kotun ta ayyana Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gabata a watan Fabrairu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kotu ta ayyana ministan Tinubu a matsayin zaɓabben sanatan Filato ta Kudu
Kotu ta ayyana ministan Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen Filato ta Kudu. Hoto: Simon Bako Lalong
Asali: Facebook

Kotu ta ayyana Lalong matsayin sabon sanatan Filato

Simon Lalong, wanda shi ne darakta janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a kakar zaɓen bana, na daga cikin gwamnoni bakwai da suka sha maye a takarar sanata.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Zaben NASS Ta Tsige Ƙarin 'Yan Majalisun Tarayya 2, Ta Ba APC da APGA Nasara

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai a ranar Litinin ɗin nan ne kotu zaɓen a zaman da ta gabatar, ta soke nasarar Napoleon Bali, inda ta kuma ayyana Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Napoleon Bali dai ya yi takarar ne a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, inda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, saɓanin Lalong na APC.

Kotu ta karɓe kujerar ɗan majalisa a jihar Filato

Har ila yau dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta karɓe kujerar ɗan Majalisar Wakilai Peter Gyendeng na jam'iyyar PDP, da ke wakiltar mazaɓar Barikin Ladi/Riyom.

Kotun ta miƙa kujerar ga Fom Dalyop na jam'iyyar Labour, wanda shi ne ya zo na biyu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu da ya gabata.

A rahoton baya na Legit Hausa, kotun ta bayyana cewa rashin cika wasu sharuɗan zaɓe ne ya janyowa jam'iyyar ta PDP rasa kujerar ɗan majalisar na ta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Dan Majalisar Jam'iyyar PDP a Arewa, Ta Ba Dan Jam'iyyar LP Nasara

Kotu ta tabbatarwa sanatan PDP kujerarsa a Benue

A wani labarin mai alaƙa da wannan da Legit Hausa ta wallafa, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen da ke zamanta a Makurdi babban birnin jihar Benue, ta tabbatar da nasarar sanatan PDP.

Kotun ta tabbatar da nasarar Abba Moro na PDP, inda ta yi watsi da ƙorafin da Daniel Onjeh na jam'iyyar APC ya shigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel