Ministan Shugaba Tinubu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara

Ministan Shugaba Tinubu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara

  • Tsohon Gwamnan Filato ya shiga tsaka mai wuya kan matsayin da ya kamata ya zaba tsakanin Minista da Sanata bayan hukuncin Kotu
  • Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta ayyana Simon Lalong a matsayin zaɓaɓɓen Sanatan Filato ta kudu, ta kori ɗan takarar PDP
  • Da yake martani kan lamarin, Lalong ya ce har yanzun yana kan shawari da mutanen mazaɓarsa kan muƙaman biyu

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Bako Lalong, ya ce har yanzun bai yanke shawarin aje muƙamin Minista ya koma Sanata ko akasin haka ba.

Ministan Kwadago, Simon Bako Lalong.
Lalong Ya Shiga Matsala Kan Mukamin Minista da Sanatan Filato Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya faɗi haka ne bayan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta ayyana shi a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen Sanatan jihar Filato ta kudu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin magoya bayan APC da PDP kan abu 1, shugaban jam'iyya ya raunata

Kotun ta tsige Sanata Napoleon Bali na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 148,844 bisa hujjar cewa PDP ba ta da halastaccen tsari, don haka haramun ne ta tsaida ƴan takara a doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lalong na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya zo na biyu da ƙuri'u 91,674 a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Wane hukunci Lalong ya yanke kan kujerun biyu?

Ya ce har yanzu yana tattaunawa da al’ummar mazabarsa kan ko zai ci gaba da zama a matsayin minista ko kuma ya koma kujerar Sanata.

Mai magana da yawun Ministan, Dakta Makut Simon Macham, shi ne ya bayyana haka yayin da yake martani kan wace kujerar tsohon Gwamnan Filato ya zaɓa bayan hukuncin Kotu.

Macham ya ce:

"Ministan kwadago da samar da ayyukan yi kuma tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya miƙa nasara ga Allah bisa tabbatar da shi a matsayin zababben Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta kudu."

Kara karanta wannan

A ƙarshe, An bayyana halin da tsohon Gwamnan babban Banki CBN ya shiga bayan hukuncin kotu

“Ya sadaukar da wannan nasarar ga daukacin al’ummar mazaɓar Filato ta kudu, kuma ya jaddada aniyarsa ta yi wa ƙasa hidima iya bakin ƙarfinsa."
"A yanzu yana tuntuɓa da neman shawari kan wannan nauyi da ya hau kansa kuma zai sanar da hukuncin da ya yanke a lokacin da ya dace."

Jam’iyyar APC reshen jihar, ta ce idan Lalong ya ci gaba da zama minista, jam’iyyar na da kwarin gwiwar sake lashe wani sabon zaben mazabar Sanatan Filato ta Kudu, rahoton Tribune.

Tinubu ya nemi a tsagaita wuta a Gaza

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Falasɗinu a Gaza.

Shugaban ƙasar ya buƙaci a koma teburin sulhu, a lalubo hanyar masalaha wajen kawo ƙarshen lamarin cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel