Gwamnatin Tinubu Ta Kitsa Rikicin Wike da Gwamna Fubara? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnatin Tinubu Ta Kitsa Rikicin Wike da Gwamna Fubara? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin tarayya ta tsame hannunta daga rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers a cikin ƴan kwanakin nan
  • FG ta ce bai kamata a ɗora mata alhakin rikicin da ke tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ba
  • Rikicin da ya ɓarke a jihar Rivers ya sa Wike da wasu ƴan majalisar dokokin jihar sun sa ƙafar wando ɗaya da Gwamna Fubara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, ta ce ba ta da hannu a rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Rivers.

Rikicin siyasar dai ya shafi Gwamna Siminalayi Fubara, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja da ƴan majalisar dokoki masu biyayya ga tsohon gwamnan Rivers.

Kara karanta wannan

IPPIS: Shugaba Tinubu ya sauya matakin da Buhari ya ɗauka kan jami'o'i da wasu manyan makarantu

FG ta yi magana kan rikicin Wike da Fubara
Gwamnatin tarayya ta nesanta kanta da rikicin Wike da Gwamna Fubara Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta fito ƙarara ta bayyana cewa gwamnati ba ta matsaya ɗaya da Wike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da ƴan jaridun fadar gwamnatin tarayya bayan kammala taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) da Shugaba Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Me FG ta ce kan rikicin Wike da Fubara?

Jaridar Leadership ta ce da aka tambaye shi ko gwamnatin tarayya na goyon bayan Wike kan lamarin a matsayinsa na mamba a majalisar ministocin tarayya, ministan yaɗa labaran ya amsa da cewa:

"Shi mamba ne a majalisar zartaswa ta tarayya yana da hannu a halin da ake ciki a jihar. Wannan ba zai iya zama matsayar gwamnatin tarayya ba. Ta yaya zai zama matsayar gwamnatin tarayya?"

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Rivers: Jigon APC ya yi wa Gwamna Fubara wankin babban bargo

Idris ya ƙara da cewa:

"Gwamnatin tarayya a kodayaushe tana sha’awar jin daɗin ɗaukacin jihohin ƙasar nan, kuma ta haka ne gwamnatin tarayya za ta haɗa kai da kowa da kowa a Najeriya domin tabbatar da cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan ƙasar nan."
"Amma ka san cewa abin da ya faru a Rivers ba gwamnatin tarayya ta haifar da shi ba. Matsala ce ta siyasa da ta kunno kai a jihar. Gwamnatin tarayya ba ta da hannu wajen haifar da wannan matsalar."

Jigon APC Ya Caccaki Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban riƙo na jam'iyyar APC a jihar Rivers ya caccaki kamun ludayin mulkin Gwamna Fubara.

Tony Okocha ya bayyana cewa gwamnan a maimakon ya ciyar da jihar gaba, sai ya mayar da ita ba kan yadda ya same ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel