Atiku/Obi vs Tinubu: Babban Fasto Ya Hango Hukuncin Da Kotun Koli Za Ta Yanke

Atiku/Obi vs Tinubu: Babban Fasto Ya Hango Hukuncin Da Kotun Koli Za Ta Yanke

  • Wani fasto mazaunin Abuja, Joshua Iginla, ya aike da sakon gargaɗi ga manyan jam’iyyun adawa biyu, PDP da LP
  • Iginla ya ce idan ba a kula ba, "laima za ta yage" kuma "baba da mama za su iya juya baya" - a wata alama da ke nuni da tambarin jam'iyyun biyu
  • Faston ya kuma yi hasashen cewa kotun kolin za ta yanke hukunci irin na kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa (PEPT)

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban cocin Champions Royal Assembly Ministry, fasto Joshua Iginla, ya ce muddin jam’iyyar PDP da Labour Party (LP) kansu na a rabe, to za a sake yin galaba a kansu a zaɓen 2027 mai zuwa.

Iginla ya ce rashin haɗin gwiwa tsakanin manyan jam’iyyun adawan biyu ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Yanke Hukunci a Kotunan Zabe, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Fasto ya hango rashin nasara ga Atiku/Obi a kotun koli
Fasto Iginla ya ce Atiku da Peter Obi za su yi rashin nasara a kotun koli Hoto: Mr. Peter Obi, Joshua Iginla Ministries, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

"Babu abin da zai fito daga ɗaukaka ƙarar Obi, Atiku."

Da yake jawabi ga mahalarta coci kwanan nan, Joshua ya ce Atiku Abubakar (PDP) da Peter Obi (LP) za su sha kaye a kotun ƙoli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duka ƴan takarar biyu sun ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun da ta yi watsi da kokensu a farkon watan Satumba, inda ta amince da nasarar shugaban kasa Bola Tinubu, a zaɓen 2023.

Iginla ya ce:

"Zan iya gaya muku sakamakon da za ku samu a 2027. Ku zage ni, ina magana da ku. Ba maganar kotun ƙoli ma na ke yi ba, ina magane ne a kan 2027."
"Idan ba ku haɗa kanku waje ɗaya ba, laima na iya yagewa, kuma baba da mama zasu iya juya baya. Ina magana da ku, ku caccakeni, ba na son na shahara. Amma ina so in gaya muku gaskiya, idan za ku iya zama ku hada kanku to kun shirya. Yanzu, kuna so ku je ku ƙwato haƙƙin ku, ku je ku ƙwato, babu abin da za ku samu."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023

Faston ya cigaba da cewa:

"Ba ina magana ne ta fuskar shari'a ba, ina magana ne ta fuskar wahayi. Na hango duk abin da zai faru nan gaba, na ga duk hujjojin da kuka kawo, kuma na ga dukkanin hukunce-hukuncen, har yanzu ina ganin fassarar da ta fi ta abin da kuke da shi."
"Ku rubuta ranar yau ku aje, domin idan sakamakon ya fito, za ku sani."

Fasto Ya Yi Hasashen Cafke Peter Obi

A wani labarin kuma, shugaban cocin Glorious Mount Of Possibilty, fasto David Kingleo Elijah ya yi hasashen cewa za a cafke Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP).

Faston ya yi kira ga magoya bayan tsohon gwamnan na jihar Anambra da su taya dan takararsu da addu'a don kada a tsare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel