Gwamna Mutfwang Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke a Filato

Gwamna Mutfwang Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke a Filato

  • Gwamnan jihar Filato ya nuna farin ciki bisa nasarar da ya samu kan APC a kotun sauraron ƙararrakin zabe mai zama a Jos
  • Celeb Mutfwang ya ce koken da jam'iyyar APC ke gabatarwa a gaban Kotun ɓata lokaci ne kawai amma sun san gaskiya
  • Ya ce zasu ɗaukaka ƙara kan zaben wasu 'yan majalisun jihar da Kotu ta soke bisa hujjar rashin tsarin PDP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya yaba da hukuncin Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna mai zama a Jos, wacce ta tabbatar da nasarar da ya samu.

Gwamnan ya nuna jin daɗinsa da hukuncin da Kotun ta yanke ranar Jumu'a, yana mai cewa shari'a ta yi magana da babbar murya, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang.
Gwamna Mutfwang Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke a Filato Hoto: channelstv
Asali: UGC

Kwamitin alkalai uku, a hukuncin da suka yanke da murya ɗaya sun bayyana cewa mai ƙara ya gaza gamsar da Kotu a ƙararsa saboda ba ta cancanta ba baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP a Arewa

Mutfwang ya yaba da wannan hukunci yayin da ya bayyana a cikin shirin siyasa a yau a gidan talabijin na Channels tv ranar Jumu'a, 22 ga watan Satumba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi magana kan ƙarar APC

Ya bayyana karar da jam’iyyar APC ta shigar na kalubalantar nasarar da ya samu a zaben a matsayin fasadi, bata lokaci da kuzari. A cewarsa, kotu ta kira su da masu katsalandan.

A kalamansa ya ce:

"Idan baku manta ba a baya, an tsige wasu daga cikin ‘yan majalisar jihata da na tarayya saboda rashin tsarin PDP. Alkalin farko ya tabbatar nasarar shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa."
"An kuma tabbatar da nasarar wasu 'yan majalisun tarayya saboda duk mai son gaskiya da adalci ya san cewa koken da APC da kowace jam’iyya ke yi ba kawai barna ba ce, bata lokaci ne da kuzari domin sun san gaskiya."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisa 3 Na PDP, Ta Faɗi Waɗanda Suka Ci Zaɓe

Da yake magana game da hukuncin korar wasu ‘yan majalisar PDP a jihar saboda rashin tsari a jam’iyyar, Gwamna Mutfwang ya ce alkalai za su ba da amsa yayin da aka ɗaukaka ƙara.

Sabon Gwamnan CBN Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

Mun kawo muku cewa Sabon mukaddashin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya shiga Ofis a karon farko ranar Jumu'a 22 ga watan Satumba, 2023

Mista Olayemi Michael Cardoso, ya karɓi rantsuwar kama aiki tare da mataimakan gwamna 4 a hedkwatar CBN da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262